Yankin jihar Adamawa inda jama'a ke shan ruwa daya da dabbobinsu

Yankin jihar Adamawa inda jama'a ke shan ruwa daya da dabbobinsu

- Da rashin muhimman gine-gine masu amfani, Folwoya Goriji, wani gari a jihar Adamawa, na fuskantar kangin rayuwa

- A garin babu tsaftataccen ruwan sha wanda hakan yasa mazauna garin ke shan ruwa a kogi daya da dabbobinsu

- Mazauna yankin, yayinda suke korafi, sun bukaci a kawo masu dauki saboda suna tunanin an manta da su

Folwoya Goriji, wani garin manoma a yankin Ndikong da ke karamar hukumar Mayo Belwa na jihar Adamawa, na da hanyar samun ruwa guda daya ne tal. Abun bakin ciki, a wuri guda mutane da dabbobi ke samun ruwan sha.

A cewar The Pilot, wannan garin sun dogara ne a kan ruwan kogo wajen gudanar da harkokinsu na yau da kullun, sannan sun yarda cewa wakilan jiharsu da na hukumarsu sun watsar da su.

Al’umman kauyen na rokon gwamnatocin jiha da na kananan hukumomi su share masu hawayensu daga illar da ke tattare da shan ruwa a waje guda da dabbobinsu.

Yankin jihar Adamawa inda jama'a ke shan ruwa daya da dabbobinsu
Yankin jihar Adamawa inda jama'a ke shan ruwa daya da dabbobinsu Hoto: Legit.ng
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Hoton kafin aure ya jawa saurayi da budurwa caccaka a wajen yan Najeriya

An kawo Baba Musa, wani mazaunin kauyen, ya na fadin cewa:

“A lokacin yakin neman zabe ne kawai muke ganinsu (yan siyasa) tare da alkawaransu na bogi da karya. Don Allah, kalli ruwan da muke sha tare da dabbobinmu kamar an manta da mu.

“Dan Allah ku fada masu kokenmu,” yan asalin garin.”

Da yake martani ga koken Musa, wani mai kare hakkin dan adam, Ibrahim Makejo, ya bayyana cewa ba garin kadai bane domin akwai saura da ke fuskantar irin wannan wahala ta rayuwa.

Yankin jihar Adamawa inda jama'a ke shan ruwa daya da dabbobinsu
Yankin jihar Adamawa inda jama'a ke shan ruwa daya da dabbobinsu Hoto: Legit.ng
Asali: UGC

Ya ce:

“Ruwan sha mai inganci, gyara da tsafta na daga cikin hanyoyi biyar na dakile cututtuka.

“Saboda haka yana da muhimmanci zababbun shugabanninmu su samar da ruwa mai inganci, da tabbatar da tsaftar muhalli da na jiki a yankunan karkara.

Legit.ng ta yi kokarin samun kansila da ke wakiltan yankin amma abun ya ci tura domin an ce baya gari.

KU KARANTA KUMA: Fayose ya ce FG za ta hukunta yan majalisar da suka aika sammaci ga Buhari kan rashin tsaro

Yankin jihar Adamawa inda jama'a ke shan ruwa daya da dabbobinsu
Yankin jihar Adamawa inda jama'a ke shan ruwa daya da dabbobinsu Hoto: Legit.ng
Asali: UGC

Yunkurin jin ta bakin Shugaban karamar hukumar ma bai haifar da yaya masu idanu ba.

A wani labarin, mun ji cewa bukatar amfani da sojojin haya wajen yaki da Boko Haram ya samu goyon baya daga shahararrun mutane.

Musamman, gwamnoni daga arewa maso gabas sun rungumi wannan kira wanda Gwamna Zulum ya fara yi.

A cewarsu, ta hakan ne kadai za a iya yin nasara a yaki da ake yi da yan ta’adda.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel