Halima Abubakar: Likita yar arewa da ke neman miji a shafin soshiyal midiya

Halima Abubakar: Likita yar arewa da ke neman miji a shafin soshiyal midiya

- Wata likita yar Najeriya mai suna Dakta Halima Abubakar ta je shafin soshiyal midiya don neman mijin aure

- Matashiyar budurwar ta wallafa wani kyakkyawan hotonta a shafinta na Twitter sannan ta tambayi mabiyanta ko suna bukatar matar aure

- Tuni bangaren sharhi na wallafar tata ya cika da martani daga mazan Najeriya wadanda suka nuna ra’ayi a kanta

Wata likita daga yankin arewacin Najeriya ta je shafin soshiyal midiya don neman mijin aure, ta wallafa hotonta a shafinta na Twitter sannan ta tambayi mabiyanta ko suna bukatar matar aure.

Dr. Halima Abubakar tare da shafin Twitter @DrHalima_ ta sa mabiyanta tattaunawa kan kyakkyawan hotonta wanda ta wallafa tare da rubutu kamar haka:

“Wa ke bukatar matar aure?”

Halima Abubakar: Likita yar arewa da ke neman miji a shafin soshiyal midiya
Halima Abubakar: Likita yar arewa da ke neman miji a shafin soshiyal midiya Hoto: @DrHalima_.
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Birtaniya ta garkame faston Najeriya da ya shahara a gagarumar damfarar 'ilimi'

Wani mai amfani da Twitter @AHMEDJEEKA ya rubuta:

“Ina ganin ba daidai bane tallata kanki a idon duniya kina neman abokan rayuwa, haramun ne a Musulunce. Mutum irina ina bukatar matar aure amma da irin wannan tallar, ina tsoro.”

@makoloumar1 ya wallafa:

“Shin za ki auri talaka mai kishin nema? + zan iya ciyar dake da baki kulawa sannan zan ba farin cikinki da kwanciyar hankalinki muhimmanci.”

@HerbertTruth ya yi martani da:

“Ina a hanyar zuwa gidan mahaifinki. Zan zo da magabata na yanzu haka. Babu lokaci.”

Ga sauran sharhin da aka yi:

KU KARANTA KUMA: Sarkin Ife ya kafa gidauniyar da za ta rika hidimar karatun miliyoyi a Jami’o’i

A wani labarin, wani saurayi dan Najeriya ya bayyana yadda budurwarsa ta auri abokinsa bayan ya hadata da shi don ya bata wuri ta kwana a Warri, lokacin da taje wani neman aiki a garin.

A wata wallafa da wani Ikhuoria yayi a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, ya ce budurwarsa ta je Warri, jihar Delta don neman aiki, sai ta kira shi tana bukatar ya samar mata wurin da za ta zauna.

A cewarsa, sai da ya bai wa budurwar ta sa kudin motan tafiyar, tukunna ta kama hanya. Maimakon ta mayar da hankalinta wurin neman aikin, sai tayi iyakar kokarinta wurin jan hankalin abokinsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng