A cikin sa’o’i 17, budurwa ta tashi daga Legas zuwa Onitsha ta koma Legas a babur

A cikin sa’o’i 17, budurwa ta tashi daga Legas zuwa Onitsha ta koma Legas a babur

- Wata shahararriyar yar Najeriya mai tuka babur, Fehintoluwa Okegbenle, ta kammala tafiyarta daga jihar Legas zuwa Onitsha sannan ta dawo cikin sa’o’i 17

- Fenitoluwa ta bayyana tafiyan a matsayin wanda babu shiri, cewa ta bar gida ne da misalin karfe 5:00 na asubahi

- Matukiyar babur din ta yi martani a kan damuwar mutane game da rashin tsaro, cewa tana sha’awar yin tafiye-tafiye a kan babur dinta

Wata matashiyar budurwa yar Najeriya da ta zama shahararriya saboda iya tukin babur, Fehintoluwa Okegbenle, ta sake nuna bajinta.

Ku tuna cewa wannan matashiyar dai a baya ta tuka babur daga jihar Legas zuwa Benin cikin sa’o’i shida yan makonni da suka gabata.

Kafin tayi tafiya, bata sanar da kowa shawararta na yin wannan tattaki ba domin ita kadai ta tafi abinta, inda ta dauki wasu ayaba, tufa da ruwa don halin tafiya.

A cikin sa’o’i 17, budurwa ta tashi daga Legas zuwa Onitsha ta koma Legas a babur
A cikin sa’o’i 17, budurwa ta tashi daga Legas zuwa Onitsha ta koma Legas a babur Hoto: @FehinLean
Source: Twitter

Kafin nan, tayi amfani da sa’o’i 13 wajen kammala tafiya daga Legas zuwa Abuja, lamarin da shine ya fara janyo hankalin mutane a kanta.

KU KARANTA KUMA: Za a daure bawan Allah da ya bindige zakara

A wannan karon, Fehintoluwa ta tuka babur dinta daga Legas zuwa Asaba sannan ta karasa Onitsha, ta kuma dawo duk a rana daya.

Da take wallafa jawabi game da tafiyarta a Twitter, ta wallafa hotuna da ke nuna lallai ta je wadannan wurare.

A cewarta, bata shirya ma tafiyar ba, inda ta kara da cewa wannan ya buge wanda tayi zuwa Abuja.

Da take martani ga wadanda suka nuna damuwa kan rashin tsaro a hanyoyin Najeriya, shahararriyar matukiyar babur din tace ta fahimci hakan amma wannan tafiye-tafiye shine muradinta.

Ga wallafar da tayi a kasa:

Ga wasu daga cikin sharhin da mutane suka yi:

@YesMyro yace:

“Nan gaba dani da ke za mu yi tafiyan... Zan kasance a baya rike dake sosai sannan na rufe idanuna.”

@Solyte_M yace:

“Kina da kamara a jikinki? Ina ganin ya kamata ki sanwa babur dinki kamara. Don nadar tafiyanki. Kina iya bude shafin YouTube idan baki da shi, ki wallafa bidiyonki, da samun kudi daga abunda kika fi son yi. Da dama daga cikinmu za mu ga yadda tafiye-tafiyen suka kasance a zahiri.”

@LADY__Beee ta ce:

“Ma shaa Allah, yayi kyau Fehintoluwa, dan Allah ki tsare kanki. Amma, dan Allah awa nawa daga Asaba zuwa Onitsha?"

KU KARANTA KUMA: Yan Najeriya sun caccaki Zulum kan cewa da yayi tsaro ya inganta a Borno karkashin Buhari

A wani labarin kuma, wata matashiyar budurwa mai suna Hafsat Samaila tare da shafin Twitter @Oummieeh ta koka a kan gajiya da zaman kadaici babu aure.

Matashiyar wacce ta fito daga yankin arewacin kasar ta roki mabiya shafin sadarwa ta Twitter a kan su taya ta rokon mahaifinta kan yayi mata aure domin a cewarta a yanzu babu abunda take so sama da hakan.

Hafsat ta kuma jaddada cewa a shirye take tayi zaman aure koda kuma na dole za a yi mata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel