Likitoci sun yanke kunnen wata mata yayin tiyata a hanci

Likitoci sun yanke kunnen wata mata yayin tiyata a hanci

- Likitoci sun yanke kunnen wata mata yar kasar China yayin tiyata don yiwa hancinta kwaskwarima

- Da fari matar mai suna Zhao bata lura da aika-aikar da likitocin suka yi ba sai bayan kwanaki hudu da yin aikin

- Ta gano pacin da aka yi wa kunnen nata ne bayan ta yi kokarin saka na'urar jin sauti amma sai yaki zama inda ya dungi zamowa

Wata mata da ta je tiyatar gyaran hanci ta shiga alhini bayan likitoci sun zabtare wani bangare na kunnenta don yin amfani da shi a hancin nata.

Matar wacce aka ambata da suna Zhao, ta kuma gano cewa na’urar jin sauti na kunne na ta fadowa daga kunnenta a lokacin da ta yi kokarin amfani dashi bayan tiyatar a Chengdu, kasar China a watan Satumba.

Matashiyar mai shekaru 31 ta yi tiyatar gyaran hanci shekaru biyar da suka gabata sannan ta yanke shawarar sake yin wani, inda ta kashe kimanin £5,700, wata kafar labarai ta China ta ruwaito kamar yadda jaridar The Sun ta kawo.

Likitoci sun yanke kunnen wata mata yayin tiyata a hanci
Likitoci sun yanke kunnen wata mata yayin tiyata a hanci Hoto: @TheSun
Source: Twitter

An tattaro cewa an shafe tsawon wasu sa’o’i ana mata tiyatar sannan an cimma nasara.

KU KARANTA KUMA: Ku tashi tsaye ku kare kanku daga yan ta’adda, kungiyar CNG ga yan arewa

Zhao ta bayyana cewa ta ji dadi bayan aikin sannan bata lura da kowani bakon abu ba har sai bayan kwanaki hudu lokacin da ta lura cewa kunnenta ba kamar yadda ta saba jinsa ba.

Daga nan sai ta gano cewa babu wani bangare na kunnenta har ciki, an cire shi a yayin yi mata tiyata ba tare da saninta ba.

Zhao ta ce ta cika da mamakin cewa likitan na iya aikata abu makamancin haka ba tare da izininta ba.

A nan take sai ta kira layin wayar masu kula da jama’a na asibitin sannan ta aika masu hotunan kunnenta.

An tattaro cewa asibitin sun ce ba wani bakon abu bane cewa cire wani bangare na kunnen ta na baya zai iya haddasa matsala, saboda haka likitoci suka dibi na ciki.

Matashiyar ta ce ta tuntubi likitoci da dama a asibitocin da ke irin wannan aiki inda suka tabbatar mata da cewa na bayan kunne aka fi amfani da shi wajen aikin kuma cewa baya shafar yanayi ko aikin kunnen.

KU KARANTA KUMA: Tsohon gwamnan Cross River Duke ya ce mayakan Boko Haram na samun makamai daga jami’an tsaro

Yuan, mataimakin Shugaban asibitin, ya bayyana cewa Zhao ta bayar da izininta ta hanyar sanya hannu a yarjejeniya kafin aikin.

Kuma cewa takardar ta bayyana cewa za a yi amfani da naman kunnenta, wanda hakan ke nufin gaba daya kunnen.

A yanzu Zhao bata iya amfani da na’urar sauti na kunne sannan cewa tana jin kunyan yadda kunnen ya koma.

Ta bukaci asibitin ya dawo mata da cikakken kudinta, diyya da kuma sake mata tiyata don gyara kunnen.

An yi zargin cewa asibitin sun ki amsa wannan tayi nata inda lamarin ya zama rikici, har yan sanda sun shiga ciki.

A gefe guda, sananniyar jarumar Nollywood, Iheme Nancy, ta nuna tsananin kaunarta ga karenta, inda ta nuna tsananin rikon amanarsa har ya zarce na wasu kawayenta.

A wata wallafa da tayi a shafinta na Instagram a ranar Juma'a, 21 ga watan Nuwamba, jarumar tace zata iya jure shirmen karenta fiye da na wasu kawayenta.

A cewarta, karenta ya fi kawayenta da dama.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel