A ƙarshe: Kotu ta garƙame mutane 6 da aka same su da ɗanyen naman mutum

A ƙarshe: Kotu ta garƙame mutane 6 da aka same su da ɗanyen naman mutum

- Kotu ta tsare wasu mutane shida da aka samu da naman mutum a garin Osogbo

- An dai zargin mazajen da kokarin amfani da gawar wani mutum don yin kudin asiri

- Sai dai sun ki amsa laifin da ake tuhumarsu a kai

Wata kotun majistare da ke Osogbo, babbar birnin jihar Osun, a ranar Alhamis, ta tsare wasu mazaje su shida, Ogunwole Lukman, Jimoh Saheed, Ogunwola Isiaka, Olawale Sodiq, Lukman Oyeyemi da Muidini Akanji kan zargin samunsu da naman mutum.

Dan sanda mai gabatar da kara, ASP John Idoko ya fada ma kotu cewa, wadanda ake zargin sun aikata laifin ne a ranar 20 ga watan Satumba, da misalin karfe 10:30 na safe a Dagbolu, hanyar Oba da ke Osogbo.

KU KARANTA KUMA: Ganduje ya amince da nadin manyan sakatarori 4 a jihar Kano (jerin sunaye)

A ƙarshe: Kotu ta garƙame mutane 6 da aka same su da ɗanyen naman mutum
A ƙarshe: Kotu ta garƙame mutane 6 da aka same su da ɗanyen naman mutum Hoto: @vanguardngrnews/@dailytrust
Source: Twitter

Idoko ya fada ma kotun cewa wadanda ake zargin sun yi wadaka da gawar wani marigayi Salami Adisa da kudirin yin kudin asiri da shi, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Dan sandan ya bayyana cewa laifin da suka aikata ya saba doka kuma hukuncinsa na a karkashin sashi na 516, 430 da 242(1)(b) na dokar jihar Osun, 2002.

KU KARANTA KUMA: Ba Kanal Baƙo kaɗai aka kashe ba: Dakarun soji sun nuna fushi kan ware sauran sojoji

Wadanda ake zargin basu amsa laifin da ake tuhumarsu a kai ba sannan lauyoyinsu, Taofeek Ibikunle da Tunbosun Oladipupo sun nemi a bayar da belinsu.

Mai shari’a Ishola Omisade ya tsare wadanda ake zargin a gidan gyara hali na Ilesa sannan ya dage shari’an zuwa ranar 30 ga watan Satumba.

A wani labarin, wani matashi mai suna Olamilekan Ibidokun, ya bada labarin yadda 'yan kungiyar asiri da ke Legas suka mayar da shi makaho bayan ya ki shiga cikinsu.

Kamar yadda yace, lamarin ya faru a watan Disamban 2016 yayin da suka yi wani shagalin biki a yankin Ketu ta jihar Legas, Vanguard ta wallafa.

Ya yi ikirarin cewa, maharan da suka makantar da shi har a halin yanzu suna yawonsu a titi ba tare da an tabbatar da wani lamari adalci a kansu ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel