Bola Tinubu
Fadar shugaban kasa ta ce ba wanda ya hana mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima shiga fadar Aso Villa. Ta ce labarin ba shi da asali bare tushe.
Ministan Abuja Nyesom Wike ya ce ya so a ce an tsige gwamna Siminalayi Fubara daga kujerar gwamna sai Bola Tinubu ya cece shi. Ya ce Fubara bai nemi shi ba.
Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya bayyana cewa ko kaɗan bai ci amanar PDP don bayyana shirinsa na marawa shugaban kasa, Bola Tinubu baya a 2027.
Tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban kasa a inuwar LP, Yusuf Datti Baba Ahmed ya ce alamu sun nuna APC ba za ta kai labari ba, ya shawarci Tinubu ya hakura.
Gwamnatiɓ Tarayya karkashin Bola Ahmed Tinubu ta bayyana shirinta na gina tashoshin samar da wuta daga hasken rana wanda aka fi sani da sola a jihohi 19.
Hoton da ake yaɗawa na Rabiu Kwankwaso sanye da hula mai ɗauke da tamabarin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ba gaskiya ba ne, kirkirarsa aka yi.
Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya ga laifin masu cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ba shi da amfanin komai wajen ciyar da shiyyar Arewa gaba.
Mataimakin shugaban kasa, Shettima ya kaddamar da kwamitin kirkire-kirkire domin rage shigo da kaya da 50%, da gina tattalin arziki mai dogaro da fasaha a Najeriya.
Tsohon ministan Buhari, Abubakar Malami ya ce bangaren CPC da Tanko Al-Makura ya ce suna goyon bayan Bola Tinubu bai tattauna da su ba, ya ce bai koma SDP ba.
Bola Tinubu
Samu kari