Rashin Tsaro: Gwamnatin Tinubu Ta Shirya Daukar Dubban Sojoji a Najeriya

Rashin Tsaro: Gwamnatin Tinubu Ta Shirya Daukar Dubban Sojoji a Najeriya

  • Rundunar sojin Najeriya ta sanar da shirin daukar sababbin sojoji domin kara yawan jami’anta da kuma karfafa yaki
  • Babban Hafsan Soji ya ce an bude sabon sansanin horas da dakaru a Amasiri Edda, wanda zai taimaka wajen horar da karin matasa
  • Sojoji sun ce suna fadada rundunoni, amfani da sababbin fasahohi da inganta jin dadin jami’ai domin kara nasara kan ‘yan ta’adda da masu laifi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana aniyarta ta daukar tare da horas da karin sababbin sojoji a Najeriya domin inganta tsaro.

Rundunar sojoji ta ce za ta dauki mutane 28,000 domin kara karfin ma’aikata da kuma inganta ayyukan yaki da matsalolin tsaro a sassan kasar nan.

Za a dauki sababbin sojoji a Najeriya
Hafsan sojojin Najeriya, Laftanar janar Waidi Shaibu. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Twitter

Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja gabanin bikin Ranar Sojojin Najeriya ta shekarar 2026, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Kano ta yi zarra, ta fi dukkan jihohin Najeriya sababbin masu rijistar katin zaɓe

Musababbin shirin kara dakarun sojoji

Ta bakin Babban Jami’in Tsare-tsare da Manufofi na rundunar, Manjo Janar Bamidele Alabi, Shaibu ya ce an samu wannan ci gaba ne bayan kafa sabon sansanin horas da dakaru a Amasiri Edda.

Ya bayyana cewa sabon sansanin ya zama cibiyar horaswa ta uku da ke shirya matasa masu koshin lafiya domin shiga aikin soja, lamarin da zai taimaka wajen kara yawan jami’an rundunar.

A cewarsa, karfin ma’aikata yana da muhimmanci kamar kayan aikin yaki, don haka rundunar ta fadada tsarin daukar ma’aikata domin tinkarar matsalolin tsaro da ke addabar kasar.

Ya kara da cewa rundunar ta samar da karin wasu sababbin sassa na aiki tare da sake duba tsarin tura jami’ai domin cike gibin da ake fuskanta.

Ana shirin daukar matasa da dama aikin soja
Ministan tsaron Najeriya, Christopher Musa. Hoto: Gen CG Musa.
Source: Twitter

Kokarin da rundunar sojoji ke yi

Babban hafsan ya ce rundunar na kara karfinta ta hanyar amfani da sababbin kayan aiki, fasahohin zamani da kuma hadin gwiwa da abokan hulda domin inganta ayyukan tsaro.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: PRP ta kawo cikas a shirin ƙirƙiro rundunar 'yan sandan jihohi a Najeriya

Haka kuma, ya ce rundunar ta bullo da tsare-tsaren karrama jarumai, inganta walwalar jami’ai da iyalansu tare da gudanar da manyan ayyukan gine-gine a sansanoni daban-daban, cewar Daily Post.

Shaibu ya bayyana cewa manufarsa ita ce gina rundunar soja mai kwarewa, jajircewa da kuma cikakken shiri wajen sauke nauyin kare kasa cikin hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro.

Ya ce sojojin Najeriya na ci gaba da gudanar da ayyuka a fadin kasa, inda suka samu nasarori wajen dakile hare-haren Boko Haram, ISWAP, masu garkuwa da mutane, ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka.

Sojoji sun musanta tilasta matasa shiga aiki

A baya, an ji cewa rundunar sojojin Najeriya ta fitar da sanarwa, domin wayar da kan al'umma kan jita-jitar cewa za ta tilasta wa matasa shiga aikin soja a kasar.

An danganta jita-jitar da cewa Laftanar-janar Waidi Shuaibu ne ya yi ikirarin tilasta matasa shiga soja, sai dai rundunar ta fito ta yi bayani.

Sanarwar da rundunar ta fitar ta jawo martani daga jama’a, inda wasu suka nemi sojoji su maida hankali kan matsalolin tsaro da ya addabi mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.