Sabuwar Kungiyar 'Yan Ta'adda Ta Shigo Arewacin Najeriya? 'Yan Sanda Sun Gano Gaskiya

Sabuwar Kungiyar 'Yan Ta'adda Ta Shigo Arewacin Najeriya? 'Yan Sanda Sun Gano Gaskiya

  • Rundunar ‘yan sandan Kebbi ta ce ta fara bincike kan rahotannin sake bullar kungiyar “Sai Malam” da ake alakantawa da ta'addanci a Argungu
  • Ta bayyana cewa tana tantance bayanan da ta samu, tana mai cewa ba a ayyana kungiyar “Sai Malam” a matsayin kungiyar ta’addanci ba
  • Rundunar ta bukaci jama'a su kwantar da hankalinsu tare da bai wa jami’an tsaro hadin kai a kokarin da suke tabbatar da zaman lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kebbi, Nigeria - Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta bayyana cewa ta fara gudanar da bincike kan rahotannin da ke cewa kungiyar “Sai Malam” ta sake bayyana a karamar hukumar Argungu.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar 'yan sanda, SP Bashir Usman, ya fitar ranar Juma'a, 26 ga watan Yuni, 2026.

Kara karanta wannan

Wata 'yar sanda ta jefa kanta a shari'ar N300m a Abuja, kotu ta sa a kamo ta

Yan sanda.
Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya a bakin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Ya ce rundunar 'yan sanda na sane da rahotannin da ake yadawa kuma tana tattara sahihan bayanai domin tabbatar da hakikanin abin da ke faruwa, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

'Sai Malam' kungiyar ta'addanci ce?

Rundunar ta yi karin haske cewa har zuwa yanzu babu wata doka ko umarnin gwamnati da ya ayyana kungiyar “Sai Malam” a matsayin kungiyar ta’addanci.

Ta ce saboda haka ana ci gaba da gudanar da bincike bisa tsarin doka domin gano ko kungiyar na da wata alaka da ayyukan ta'addanci ko sauran laifuffuka.

A cewar rundunar, wasu da ake zargi da hannu a ayyukan kungiyar sun taba shiga hannu kuma aka gurfanar da su a kotu a watan Fabrairun shekarar 2026 a Zuru.

Abubuwan da bincike ya gano

Ta bayyana cewa binciken da aka gudanar a lokacin ya sa aka kwato wasu abubuwa da ake zargi na haramtattun ayyuka ne.

Daga cikin kayayyakin da aka samu akwai kudaden jabu na kasashe daban-daban, ciki har da Naira ta Najeriya, Dalar Amurka, CFA Franc da Dinar na Libya.

Kara karanta wannan

Bayan Boko Haram, ISWAP da Lakurawa, sabuwar kungiyar 'yan ta'adda ta bayyana a Arewa

Haka kuma an kwato wasu kayayyakin da ake zargin ana amfani da su wajen tsafe-tsafe ko wasu al'amuran sihiri, da sauran kayayyaki masu alaka da binciken.

Sai dai rundunar ta jaddada cewa babu wata bindiga ko makamin harbi da aka samu a hannun wadanda ake zargin yayin gudanar da binciken, cewar rahoton PM News.

Kebbi.
Taswirar jihar Kebbi da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

An bukaci mutane su kwantar da hankula

Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta sake tabbatar da kudirinta na kare rayuka da dukiyoyin al'umma tare da daukar matakin doka kan duk wani nau'in laifi.

Ta kuma bukaci mazauna jihar su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen gudanar da bincike da kuma dakile ayyukan ta'addanci.

Yan sanda sun bayani kan bidiyo

A wani labarin, kun ji cewa rundunar ‘yan sandan Najeriya (NPF) ta karyata rahotannin da ke yawo cewa wasu jami’anta suna mu’amala ko hada kai da ‘yan bindiga a jihar Katsina.

Hakan na zuwa ne bayan wani bidiyon da ya karade kafafen sada zumunta ya nuna ‘yan sanda suna gaisawa da wasu dauke da makamai a kan babura kuma suka bar su suka wuce.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, ACP Anietie Iniedu, ya fitar ranar Laraba, ya bayyana cewa mutanen da aka gani a bidiyon ba ‘yan bindiga ba ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262