Zaben 2027: Gwamna Sule Ya Fadi Abin da Yankin Arewa Zai Yi Wa Shugaba Tinubu
- Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya bayyana cewa yankin Arewa zai sake zaɓar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027
- Abdullahi Sule ya bayyana cewa yankin Arewa ba zai saɓa da alƙawarin da ya ɗauka ba na goyon bayan ɗan Kudu domin zama shugaban ƙasa
- Gwamnan ya bayyana nuna cewa akwai ƴan siyasa da ke ƙoƙarin kawo ruɗani domin cimma wasu muradunsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Nasarawa - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi magana kan goyon bayan da yankin Arewa zai ba Shugaba Bola Tinubu a 2027.
Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana cewa yankin Arewa ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen goyon bayan sake zaɓen Shugaba Tinubu a shekarar 2027.

Asali: Twitter
Jaridar The Nation ta ce ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a bikin Nzeh Mada na shekarar 2025 da aka gudanar a Akwanga, ƙaramar hukumar Akwanga ta jihar Nasarawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Abdullahi Sule ya ce kan zaɓen 2027?
Gwamna Abdullahi Sule ya ce lokaci ya yi da ya zama wajibi ga Arewa za ta dage domin ganin Tinubu ya dawo kan mulki a shekarar 2027.
Ya ce, goyon bayan sake zaɓen shugaban ƙasan zai zama cika alƙawarin da manyan shugabannin Arewa suka ɗauka kafin babban zaɓen 2023.
Gwamna Abdullahi Sule, wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewa ta Tsakiya, ya ce Arewa ba ta da tarihin saɓa alƙawari.
Ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a Arewa da su yi watsi da ƙoƙarin wasu ƴan siyasa da ke ƙoƙarin haifar da rikici saboda gaza cimma muradunsu na ƙashin kansu.
Ya ce waɗannan ƴan siyasa su ne a da suka tsaya tsayin daka wajen tallata Tinubu a Arewa a shekarar 2023.
“Wasu ƴan siyasa idan ba su samu abin da suke nema ba, sai su haddasa ruɗani da fitina."
“A lokacin da nake farkon zama a matsayin gwamna, wasu daga cikin tsofaffin gwamnoni sun ce mutum mafi cancanta don shugabancin Najeriya shi ne Bola Ahmed Tinubu."
“Sun ce Tinubu zai iya sauya Najeriya kamar yadda ya sauya Legas zuwa cibiyar kasuwanci da tattalin arziƙi."
“Lokaci ne mai cike da ƙalubale, amma muka dage har muka taimaka muka kai shi kan kujerar shugaban ƙasa."
"Yau kuma, waɗancan mutane saboda ba su samu muradunsu ba, sun fara sukar Tinubu, suna cewa shi ne shugaban ƙasa mafi muni da Najeriya ta taɓa yi."
"To, ko da kuwa mai kyau ne, ko mara kyau, ko akasin haka, da ikon Allah, za mu dawo da Bola Ahmed Tinubu ya ci gaba da jagorantar Najeriya."
Gwamna Sule ya ce Arewa za ta mutunta alƙawari
Ya ƙara da cewa Arewa ta riga ta amince da cewa tun da ta riƙe mulki na tsawon shekara takwas, lokaci ne da mulki zai koma yankin Kudu.

Asali: Facebook
“Don haka, ba za mu saɓa da abin da muka faɗa ba. Ba za mu ce abu guda yau, gobe kuma mu ce wani ba."
"Dole ne mu zama masu haƙuri, mu ba shugaban ƙasa damar kammala shekara takwas a ofis."
- Gwamna Abdullahi Sule
An shawarci Tinubu ka da ya yi takara a 2027
A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar LP a zaɓen 2023, Datti Baba-Ahmed, ya shawarci Shugaba Bola Tinubu, kan ka da ya sake tsayawa takara a 2027.
Datti ya nuna cewa idan Tinubu na da wayau a siyasance ba zai yi gangancin neman yi tazarce ba.
Ya ƙara da cewa lokaci ya ƙurewa shugaban ƙasan da jam'iyyarsa ta APC domin ƴan Najeriya za su fatattake su a 2027.
Asali: Legit.ng