2027: Ana Hasashen Haɗa Takarar Atiku da Obi, an Tsara Yadda Za Su Yi Karba Karba

2027: Ana Hasashen Haɗa Takarar Atiku da Obi, an Tsara Yadda Za Su Yi Karba Karba

  • An ce tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na shirin takara a 2027 da Peter Obi a matsayin mataimakinsa, domin kalubalantar Bola Tinubu
  • Tushen hadin gwiwar shi ne amfani da karfin Atiku a Arewa da kuma farin jinin Obi a Kudu domin gina babbar jam'iyya adawa
  • Ana hasashen Atiku zai yi wa'adin shekara hudu kawai, daga 2027 zuwa 2031, sannan ya mika mulki ga Obi wanda zai yi wa'adi biyu
  • Masu biyayya ga Obi sun ki amincewa da hadin gwiwar idan ba shi ne dan takarar shugaban kasa ba, suna kira Atiku ya mara masa baya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Yanayin siyasar Najeriya ya cika da jita-jita kan zaben shugaban kasa na 2027, musamman kan yiwuwar hadin gwiwa tsakanin Atiku Abubakar da Peter Obi.

Majiyoyi sun ce Atiku na shirin tsayawa takara tare da Peter Obi a matsayin mataimakinsa, domin su hada karfi su kalubalanci Bola Tinubu.

Ana hasashen haɗa Atiku da Obi a takarar shugabancin kasa
Yan 'Obedients' sun ki amincewa da tsarin Obi ya zama mataimakin Atiku a 2027. Hoto: Peter Obi, Asiwaju Bola Tinubu, Atiku Abubakar.
Asali: Facebook

An yi hasashen haɗa Atiku, Obi takara

Hadin gwiwar na da nufin amfani da karfin Atiku a Arewa da kuma farin jinin Obi a Kudu domin gina babbar adawa, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babban abu mai musamman a wannan shiri shi ne yarjejeniyar rabon iko inda Atiku zai yi wa'adi daya sannan ya mika mulki ga Obi.

An ce Obi zai ci gaba da mulki bayan Atiku, inda zai yi wa’adin mulki biyu daga shekarar 2031 zuwa 2039 a matsayin shugaban kasa.

Duba da PDP da LP na fama da rikicin cikin gida, ana tunanin amfani da SDP a matsayin sabuwar dandalin siyasa.

Ana shirin hada takarar Atiku da Obi a 2027
Da alama zaben 2027 zai zo da abubuwa bayan zargin haɗa Atiku da Obi takara. Hoto: Atiku Abubakar, Peter Obi.
Asali: Facebook

Matsayar yan 'Obidients' kan shirin a 2027

Sai dai, mambobin tafiyar 'Obidient' sun ce ba za su amince da kowane hadin gwiwa ba idan ba Obi ne dan takara ba.

Sun jaddada cewa duk wani shiri da ba ya kunshi Obi a matsayin dan takara ba zai yi nasara ba, kuma Atiku ya mara masa baya.

A cewarsu, bai dace Atiku ya sake tsayawa takara ba, duba da cewa yankin Kudu bai gama shekara takwas na mulki ba.

Don haka ya kamata ya ja daga, ya ba Peter Obi dama ya tsaya takarar shugaban kasa a 2027 domin tabbatar da adalci.

Daya daga cikin masu wannan ra’ayi shi ne Samuel Ajayi, wanda ya bayyana kansa a matsayin Obidient.

A cewarsa:

“Idan mun taba yin Atiku/Obi kuma bai yi ba, me ya sa ba za mu yi Obi/Atiku ba? Kada ku saka son zuciya.”

Fayose ya soki takarar Atiku a 2027

Kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose ya bayyana cewa zai yaƙi Atiku Abubakar idan ya sake tsayawa takarar shugaban ƙasa.

Fayose wanda ya yi mulki a PDP ya ce ba zai yiwu ɗan Arewa ya gama shekaru takwas kuma wani ɗan Arewa ya karbi mulkin Najeriya ba.

A cewarsa, idan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya samu nasarar zarcewa, da kansa zai fito da yaƙi duk ɗan Kudun da ya nemi mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.