"Ban Ci Amanar PDP ba," Gwamnan PDP Ya Yi Bayani kan Goyon Bayan Tinubu a 2027

"Ban Ci Amanar PDP ba," Gwamnan PDP Ya Yi Bayani kan Goyon Bayan Tinubu a 2027

  • Gwamnan Akwa Ibom ya nanata shirinsa na marawa Bola Ahmed Tinubu baya a zaɓen 2027 duk da ba jam'iyyarsu ɗaya ba
  • Fasto Umo Eno ya ce matakin da ya ɗauka ba cin amanar PDP ba ne domin kowane ɗan jam'iyya yana da ra'ayinsa na siyasa
  • Gwamnan ya ce idan lokaci ya yi, zai fito ya bayyana dalilan da ya sa yake ganin Tinubu ya cancanci damar ƙarasa ayyukan da ya fara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Akwa Ibom - Gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno, ya bayyana cewa goyon bayan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi tazarce a 2027 ba cin amanar PDP ba ne.

Gwamna Eno na jam'iyyar PDP ya ce yana sane kuma da cikakken tunani ya yanke shawarar yi wa Bola Tinubu aiki domin ya samu nasara a karo na biyu.

Gwamna Umo Eno.
Gwamna Umo Eno na Akwa Ibom ya jaddada goyon bayansa ga Bola Tinubu Hoto: Umo Eno
Asali: Facebook

Fasto Umo Eno ya yi wannan bayanin ne a wurin wani taron siyasa da aka gudanar a ƙaramar hukumar Ikot Ekpene a ranar Talata, Channels tv ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Gwamna Eno ya goyi bayan Tinubu?

Da yake bayyana wasu daga cikin dalilinsa, Gwamna Eno ya ce ya yanke wannan shawara ne cikin gaskiya da amana, kuma daga baya zai bayyana dalilansa.

“Ni ban iya magana biyu ba, ranar da na ce zan goyi bayan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, wasu sun tambaye ni ‘me ya sa?’
"Wasu munafukai ne, da daddare za su je wurin Baba su ce masa za su goyi bayansa, amma da rana su yi wata magana daban. Ni dai zan goyi bayan Baba Bola Ahmed Tinubu ya yi tazarce.
"Idan lokacin ya yi, zan faɗa muku dalilina. Amma yanzu dai zan ajiye shi a zuciyata, babu dalilin da zai sa na cuci kaina."

- Umo Eno.

Gwamna Eno ya yi maganar ayyukna Tinubu

Gwamna Eno ya ce idan lokacin ya yi, mutane za su fahimci dalilansa da kuma dalilin da ya sa ya kamata a ba Tinubu dama ya kammala abin da ya fara.

“Za ku ga abubuwan da yake yi a jiharmu, kuma za ku fahimci dalilin da ya sa bai kamata mu koma wani wuri ba. Idan kana son mu goyi bayanka, ka bari Tinubu ya gama takwas.
Bola Tinubu.
Gwamna Eno ya bayyana cewa yana nan daram a PDP Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Umo Eno
Asali: Facebook

Shin Gwamna Eno ya ci amanar PDP?

Gwamnan ya kara da cewa wannan matsaya tasa ba ta canja matsayinsa na ɗan jam’iyyar PDP ba, ma'ana yana nan daram a cikinta.

"Goyon bayan Tinubu ba zai hana ni kasancewa ɗan jam'iyyar PDP ba, ina da damar bayyana ra'ayina a siyasance."

Gwamnan ya kuma ce yana samun cikakken goyon baya a kan burinsa na neman wa’adi na biyu daga Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio.

Barau ya hango nasarar APC a 2027

A wani labarin, mun kawo cewa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin, ya bayyana cewa yana da kwarin guiwar APC za ta yi nasara a 2027.

Sanata Barau ya ce yadda ƴan adawa ke baro jam'iyyunsu suna dawowa APC alama ce da ke nuna yadda ƴan Najeriya suka gamsu da salon mulkin Tinubu.

Barau ya yi wannan kalamai ne a wurin wani taron haɗin kan ƴaƴan APC da aka gudanar a Abuja, inda aka tarbi masu sauya sheƙa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262