"Za Ka Yi Mummunar Faɗuwa," An Shawarci Tinubu Kada Ya Nemi Tazarce a Zaben 2027

"Za Ka Yi Mummunar Faɗuwa," An Shawarci Tinubu Kada Ya Nemi Tazarce a Zaben 2027

  • Abokin takarar Peter Obi a zaɓen 2023, Yusuf Datti Baba-Ahmed ya shawarci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya hakura da tazarce
  • Yusuf Datti ya bayyana cewa matukar Tinubu na da wayon siyasa kamar yadda aka shaida a baya, bai kamata ya sake neman takara ba
  • Tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasar kuma jigo a LP ya ce alamu sun nuna APC za ta yi mummunan faɗuwa a zaɓe na gaba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Yusuf Datti Baba-Ahmed, ya shawarci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da kada ya sake neman takara a zaben 2027.

Yusuf Baba Ahmed ya ce idan har Shugaba Tinubu na da wayon a siyasa, ba zai yi gigin sake neman kujerar shugabancin Najeriya ba a zaɓe mai zuwa.

Shugaba Tinubu da Yusuf Datti.
Yusuf Datti Baba-Ahmed ya shawarci Tinubu da kada ya sake neman shugabanci a 2027 Hoto: @OfficialABAT, @LabourNG
Asali: Twitter

Baba-Ahmed ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi a shirin Prime Time na gidan talabijin na Arise a ranar Juma’a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu zai hakura da neman tazarce?

Ya ce lokaci ya kure wa Tinubu, kuma akwai alamun da ke nuna cewa shi da jam’iyyarsa ta APC za su sha mummunan kaye a 2027.

A cewarsa:

"Ina tsammanin Tinubu zai janye idan da gaske shi ƙwararren ɗan siyasa ne mai wayo kamar yadda ake tsammani.”

Yusuf Baba-Ahmed ya bayyana Tinubu a matsayin “ɗan siyasa mai wayo ƙwarai,” wanda tun 2007 yake fitar da ‘yan takarar shugaban ƙasa daban-daban, har ta kai ga ya ci nasara a 2023.

Yusuf Datti ya hango faɗuwar Bola Tinubu

“Ya kauce wa 2007 ya sanya Atiku, ya sanya Ribadu a 2011, daga baya ya goyi bayan Buhari a 2015, sannan suka sake cin nasara a 2019.
"A 2023 kuma suka tafka maguɗi. Idan har yana da wannan wayon, dukkan alamu na nuna ba zai yi nasara a 2027 ba," in ji shi.

Babban jigo a LP ya kuma bayyana cewa akwai ‘yan takara guda biyu da za su iya doke Tinubu a 2027, kodayake bai bayyana sunayensu ba.

Ya ce Tinubu ba zai iya cika alkawuran da ya ɗauka ga ‘yan Najeriya ba, domin kuwa jam’iyyar APC ta tabbatar da cewa “karya ce.”

Yusuf Datti Baba Ahmed.
Jigon LP ya hango irin faɗuwar da APC za ta yi a 2027 Hoto: Yusuf Datti Baba Ahmed
Asali: UGC

Buhari da Shugaba Tinubu sun gaza

A ruwayar Vanguard, Yusuf ya ƙara da cewa:

“Buhari bai kawo ci gaba a Najeriya ba, bai samar da tsaro ba, bai yaki cin hanci da rashawa ba, haka ma Tinubu ba zai iya yin hakan ba.”

Yusuf Baba-Ahmed ya yi hasashen cewa APC za ta fadi a zaben 2027, inda ya kara da cewa ‘yan Najeriya za su haɗu wuri guda domin kawar da jagoranci maras nagarta.

Tinubu zai sake neman takara a APC

A wani labarin, kun ji cewa jiga-jigan APC na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu kan wanda jam'iyya mai mulki za ta ba tikitin takarar shugaban ƙasa a 2027.

Tsohon ɗan Majalisar Tarayya, Farouk Aliyu ya bayyana cewa babu wanda APC za ta ba takara face Shugaban Kasa, Bola Tinubu.

Ya ce za su mara wa Shugaba Tinubu baya a zaɓen 2027 kamar yadda suka yi a 2023 kuma da ikon Allah shi ne zai samu nasara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262