Duk da Tatsar N10m daga Al'umma, Ƴan Bindiga Sun Kona Makarantar Firamare Kurmus

Duk da Tatsar N10m daga Al'umma, Ƴan Bindiga Sun Kona Makarantar Firamare Kurmus

  • Yan bindiga sun kona makarantar firamare bayan sun karɓi harajin Naira miliyan 10 da suka tilasta al’ummomin yankin
  • Mazauna yankin sun ce maharan sun fito daga dajin Kainji, suka kai hari hedikwatar gundumar tare da lalata makarantar
  • A wani harin kuma, an kashe mutum ɗaya yayin da aka sace wani a hare-haren da aka kai a wasu kauyuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Minna, Niger - Majiyoyi sun ruwaito cewa 'yan bindiga sun ƙone wata makarantar firamare da ke garin Dekara a ƙaramar hukumar Borgu ta Niger.

Maharan sun ɗauki wannan matakin ne duk da cewa sun karɓi harajin Naira miliyan 10 daga al’ummomin yankin.

Yan bindiga sun kona makaranta a Niger
Taswirar jihar Niger da ke fama da hare-haren ƴan bindiga. Hoto: Legit.
Source: Original

Mazauna yankin sun shaida wa Daily Trust cewa maharan sun banka wa makarantar firamare ta 'Central', Dekara wuta ne yayin wani hari da suka kai garin.

Kara karanta wannan

'Yaran jagoran 'yan bindigan da suka sace Janar sun sake sabon ta'addanci a Katsina

Abin da mazauna yankin ke cewa

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce 'yan bindigar sun fito ne daga dajin Kainji kafin su mamaye al’ummar.

A cewarsa, ƙauyuka da al’ummomin gundumar Dekara sun haɗa kuɗi tare domin biyan Naira miliyan 10 da 'yan bindigar suka nema bayan sun yi barazanar kai hari.

Ya bayyana cewa an biya kuɗin ne bayan maharan sun yi alkawarin barin mazauna yankin su ci gaba da zama cikin ƙauyukansu ba tare da ƙarin hare-hare ba.

“'Yan bindigar sun kakaba mana harajin Naira miliyan 10, mun biya saboda sun yi barazanar kai mana hari idan muka ƙi biyan kuɗin.
“Amma duk da sun karɓi kuɗin, sun sake kai hari hedikwatar gundumar tare da ƙona makarantar firamare."

- in ji mazaunin yankin

An kona makarantar firamare a Niger
Gwamna Mohammed Umaru Bago na jihar Niger. Hoto: Gov. Mohammed Umaru Bago.
Source: Twitter

Matsalolin da jihar Niger ke ciki

Jihar Niger na daga cikin jihohin da ke fama da hare-haren yan bindiga wanda ya jawo asarar rayuka da dukiyoyin al'umma, cewar rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Babbar mota ta burma kan 'yan APC suna tafiya kamfen, an samu asarar rai

Al'umma, masu ruwa da tsaki da masu fashin baki kan harkokin yau da kullum suna nuna damuwa kan ci gaba da kashe mutane da ake yi ba kakkautawa inda suka bukaci hukumomi su kawo karshen abin da ke faruwa.

Har zuwa lokacin tattara wannan rahoton, ba a samu jin tabakin kakakin rundunar yan sandan jihar ba domin yin karin haske.

Mai magana da yawun rundunar, SP Wasiu Abiodun, bai amsa kiran waya ba, haka kuma bai mayar da martani ga saƙon tes da aka aika masa ba.

Yan bindiga sun yi wa mutane wa'azi

Mun ba ku labarin cewa wasu ‘yan ta'adda masu ikirarin jihadi sun shiga Neja tare da tara mazauna Zugurma domin gabatar da wani wa’azi mai cike da barazana.

Mazauna yankin Zugurma sun ce mayakan sun iso garin da babura kusan 30 sanye da kayan sojoji da rawani kafin su rarraba kansu domin yin wa'azi.

Ana zargin cewa 'yan ta'addar suna karkashin ƙungiyar Lakurawa ne, wacce masu nazarin tsaro ke danganta ta da ƙungiyoyin jihadi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.