Gwamnatin Tinubu Ta Kinkimo Aikin da Zai Kawo Karshen Matsalar Ɗauke Wuta a Jihohi 19

Gwamnatin Tinubu Ta Kinkimo Aikin da Zai Kawo Karshen Matsalar Ɗauke Wuta a Jihohi 19

  • Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirinta na share hawayen ƴan Arewa kan matsalar lalacewar wutar lantarki
  • Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya ce gwamnati na shirin gina sababbin tashohin samar da wuta daga hasken rana a jihohi 19
  • Hakan dai ya biyo bayan matsalolin da aka fuskanta a watannin da suka shuɗe na lalata turakun wuta da satar kayayyaki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa tana da shirin gina sababbin tashoshin samar da wutar lantarki daga hasken rana watau sola masu karfin megawat 1,900 a Arewa.

Haka kuma, gwamnatin ta bayyana kudirinta na samar da megawat 8,000 na wutar lantarki kafin karshen wa’adin farko na Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027.

Adebayo Adelabu.
Gwamnatin Tarayya ta waiwayi matsalar wutar lantarki a jihohin Arewa 19 Hoto: Adebayo Adelabu
Asali: Twitter

Ministan Makamashi, Adebayo Adelabu, ne ya sanar da haka a taron bitar ayyuka na ministoci karo na shida da aka gudanar ranar Alhamis a Abuja, rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Tinubu za ta magance ɗauke wuta

Adelabu ya ce kowace daga cikin tashoshin wuta ta sola da za a gina a jihohin Arewa 19, za ta iya samar da megawat 100.

Kuma a cewarsa, hakan zai bai wa kowace jiha damar samun 'yancin kanta wajen samar da makamashi ba tare da dogaro da na kasa gaba daya ba.

Ya kuma bayyana cewa gwamnati na kokarin jawo masu zuba jari masu zaman kansu domin fadada hanyoyin samar da wuta da gyara layukan rarrabata.

Yadda Arewa ta sha fama da lalacewar lantarki

Idan zaku iya tunawa yankin Arewa ya fuskanci matsalar yawan katsewar wuta a kwanakin baya, sakamakon yawaitar lalata kayayyakin wutar lantarki da satarsu.

A watan Oktoba na bara, wasu bata-gari sun lalata babban turken wuta na Shiroro wanda ke bai wa jihohin Kano da Kaduna wuta, da kuma wani layi da ke kai wuta zuwa Bauchi, Gombe da wasu sassan Arewa maso Gabas.

Wannan al’amari ya haifar da rashin wuta na tsawon wata guda a jihohi 17 daga cikin 19 na Arewa.

Bayan an gyara, gwamnonin yankin sun bukaci a fadada hanyoyin samar da wuta don kaucewa irin wannan matsala a nan gaba.

Jihohin da abin ya shafa sun hada da: Neja, Kwara, Kaduna, Kano, Jigawa, Gombe, Katsina, Sakkwato, Zamfara, Bauchi, Yobe da Borno.

Har ila yau akwai Adamawa, Taraba, Filato, Nasarawa, Kogi da kuma Benuwai.

Sola.
Za fara samar da wutar lantarki daga hasken rana a Najeriya Hoto: Getty Image
Asali: Twitter

Wane shiri gwamnatin tarayya ta ɗauko?

A yayin taron, Ministan ya bayyana cewa kasancewar Najeriya na da isasshen hasken rana, bai kamata ta kasa samar da wutar sola a matakin kasa ba.

"Baya ga wadannan shirye-shirye, akwai kamfanonin masu zaman kansu kamar Sun Africa Energy da Skipper Electric da ke sha'awar zuba jari a fannin wutar lantarki a Najeriya.
"Amma sun fi son zuba kudinsu a ɓangaren samar da wuta na zamani wanda ake sabuntawa akai-akai

"Da irin hasken rana da muke da shi a Najeriya, babu wani dalili da zai hana mu samun tashoshin samar da wutar na sola a matakin kasa.

- In ji Adelabu.

Adelabu ya bayyana burin gwamnatin Tinubu na samar da wutar lantarki mai ƙarfin megawatt 8,000 abu ne da zai yiwu, yana mai cewa an samu ƙarin wuta da 40% daga zuwan Tinubu zuwa yau.

Kamfanonin samar da wuta sun fusata

A wani labarin, kun ji cewa matsala da kunno kai a ɓangaren samar da wuta yayin da kamfanonin GenCos suka yi barazanar dakatar da ayyukansu a Najeriya.

Kamfanonin sun bayyana cewa za su dakatar da aiki idan har gwamnatin tarayya ta ci gaba da yin watsi da bashin Naira tiriliyan 4 da suke binta.

Shugaban kwamitin kamfanonin samar da wuta watau GenCos ya ce ba zai yiwu su ci gaba da aiki a haka ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262