Mataimakin Gwamnan Bauchi Ya Zabgawa Ministan Tinubu Mari? An Samu Bayanai

Mataimakin Gwamnan Bauchi Ya Zabgawa Ministan Tinubu Mari? An Samu Bayanai

  • Mataimakin gwamnan Bauchi, Mohammed Auwal Jatau, ya musanta zargin cewa ya mari ministan harkokin waje, Yusuf Maitama Tuggar
  • Lamarin da ake cewa ya faru a cikin bas ya haddasa cece-kuce, inda wasu ke cewa rikici ya ɓarke bayan cin fuska ga Gwamna Bala Mohammed
  • Mai magana da yawun Jatau ya ce ba a taɓa samun hakan ba a Bauchi, yana ƙalubalantar masu da’awar da su kawo hujjoji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Bauchi - Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi, Rt. Hon. Muhammad Auwal Jatau ya yi magana kan jita-jitar marin minista a jihar.

Jatau ya karyata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa ya mari Ministan Harkokin Waje, Amb. Yusuf Tuggar.

Ana zargin mataimakin gwamna da marin minista
Mataimakin gwamnan Bauchi ya musanta marin ministan Bola Tinubu. Hoto: Yusuf Tuggar, Jatau.
Asali: Facebook

An yada jita-jitar faruwar haka ne a wani babban taro da aka gudanar a jihar ranar Juma’a, cewar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin mataimakin gwamna ya mari Minista

Ana zargin lamarin ya faru a cikin wata farar bas da ke dauke da manyan baki daga Filin Jirgin Sama zuwa fadar Sarkin Bauchi.

A cewar wasu rahotanni da ba a tabbatar da su ba, rikici ya tashi ne bayan Tuggar ya furta kalaman marasa dadi kan Gwamna Bala Mohammed.

Aka ce hakan ya fusata Jatau har ya mari ministan a gaban mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da wasu manyan mutane.

Martanin Auwal Jatau kan marin Ministan waje

Amma mai magana da yawun mataimakin Gwamna, Muslim Lawal, ya musanta zargin gaba ɗaya, yana mai cewa labarin ƙarya ne marar tushe.

Muslim ya ce:

"A’a, a’a, a’a, yaya za a ce mataimakin gwamna ya mari minista? Ban yarda hakan ta faru a Bauchi ba, domin ina sane da hali na ubangidana.
"Mutum na biyu a gwamnatin jiha ba zai mari Minista ko wani mutum ba, ba mu da masaniya kan hakan, na ji ne daga gare ka yanzu."

Babu gaskiya a labarin marin minista a Bauchi
Mataimakin gwamnan Bauchi musanta rade-radin marin Minista Yusuf Tuggar. Hoto: Ministry of Foreign Affairs, Nigeria, Yusuf Ad Yusuf.
Asali: Facebook

Mataimakin gwamna ya kalubalanci masu yada karya

Lawal ya ƙalubalanci sahihancin rahoton, yana cewa duk wanda ke da hujja ya gabatar da ita don tabbatar da gaskiya, cewar Arise News.

Ya kara da cewa:

"Ka ga shaidar marin? Ni ban gani ba, ina jin ne daga gare ka. Amma ban yarda cewa mataimakin gwamna zai mari minista ba.
"Me zai sa ma mataimakin gwamna ya mari Minista? Ban kasance cikin motar ba. Idan akwai hujja za mu iya magana, amma yanzu babu.
"Ni ban san da hakan ba. Wannan shi ne matsayinmu. Kuma ko ba a gaban Mataimakin Shugaban Kasa ba, ban yarda Jatau zai yi hakan ba."

Shettima da gwamnoni sun dura a Bauchi

Kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya jagoranci tawagar gwamnoni da wasu manyan jami’an gwamnati zuwa Bauchi domin halartar nadin sarauta.

Tsohon gwamnan Bauchi ya samu sarautar Makama Babba daga fadar Mai Martaba Sarkin Bauchi, yayin da aka hada bikin da daurin auren diyarsa.

Bala Mohammed ya yaba da gudunmawar tsohon gwamnan tare da jaddada kudirin gwamnatinsa na aiwatar da ayyukan raya kasa musamman a karkara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.