Rivers: Wike Ya Fito Karara Ya Yi Magana kan Raba Fubara da Gwamna har Abada
- Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce yaso a ce an tsige gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara gaba ɗaya daga kan mulki
- Wike ya bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne ya dakile hakan ta hanyar ayyana dokar ta-ɓaci, lamarin da ya ceci Fubara
- Ministan ya nuna bacin ransa kan yadda Fubara bai nemi maslaha da shi ba, duk da rikicin da ke tsakanin su yana ƙara taɓarɓarewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Rikicin siyasar Ribas ya ɗauki sabon salo, tsohon gwamnan jihar kuma ministan Abuja, Nyesom Wike ya fito karara ya bayyana cewa yana son a tsige Simi Fubara.
Wike ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai a Abuja a ranar Juma’a, inda ya ce matakin da shugaba Tinubu ya dauka ne ya hana hakan ta faru.

Asali: Facebook
Rahoton jaridar the Cable ya nuna cewa Nyesom Wike ya ce bai ji dadin sanya dokar ta baci da Tinubu ya yi ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, matakin shugaban ƙasa na ayyana dokar ta-ɓaci da kuma dakatar da gwamnan da mukarrabansa ya hana jihar faɗawa cikin mummunan rikici.
'Tinubu ya ceci Fubara da ya dakatar da shi,' Wike
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce bai ji dadi ba sam kan matakin da shugaban kasa ya dauka na dakatar da Simi Fubara.
Wike ya ce:
“A matsayina na dan siyasa, ban ji daɗin dokar ta-ɓacin da aka ayyana a jihar Ribas ba. Na fi so a tsige Fubara gaba ɗaya, amma shugaban ƙasa ya cece shi.”
Ya ƙara da cewa:
“Ta Fubara ta kare – tabbas ya tafi, amma shugaban ƙasa ne ya ceci shi. Duk safiya ya kamata su je su ce masa, ‘Muna godiya da kubutar da mu da kayi ?’”
A cewar Wike, akwai buƙatar mutane su rika faɗin gaskiya kan yadda Bola Tinubu ya hana jihar faɗawa cikin rikici mai tsanani.
Wike ya zargi Fubara da watsi da shi
Ministan ya nuna cewa bai gamsu da halayyar Fubara ba, yana mai cewa bai taɓa kiran shi domin neman maslaha ko fahimtar juna ba tun da aka dakatar da shi.
Jaridar Punch ta wallafa cewa Wike ya ce:
“Ina tambaya, shin ko sau ɗaya ya taɓa kirana ya ce, ‘Yallaboi, me ya kamata mu yi, wane hali ake ciki?’”
Wike ya ce ko da kuwa ana cewa shi ne ke da laifi a cikin rikicin, bai dace a bari lamura su tabarbare haka ba, ba tare da kiran tattaunawa ba.

Asali: Facebook
An kafa kwamitin lura da Rivers a majalisa
A wani rahoton, kun ji cewa majalisar wakilai ta kafa wani gagarumin kwamiti mai dauke da mutane sama da 20 domin lura da harkokin majalisa a Rivers.
Shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajuddeen ne ya kaddamar da kwamitin, inda ya bukace su da su yi adalci.
Shugaban kwamitin ya tabbatar da cewa za su yi adalci wajen saka ido da lura da yadda shugaban rikon Rivers zai yi aiki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng