Sojojin Najeriya Sun Kai Farmaki Dajin Filato, Sun Yi Barin Wuta kan Ƴan Bindiga
- Dakarun Operation ENDURING PEACE sun ceto mutane takwas da aka yi garkuwa da su daga dajin Pandam da ke karamar hukumar Qua’an Pan
- Rundunar ta ce an kai farmakin ne da misalin karfe 3 na dare bayan samun bayanan sirri kan ayyukan masu garkuwa da mutane
- Sojojin sun yi musayar wuta da ‘yan bindigar yayin aikin, inda wasu daga cikin wadanda aka sace suka tsere kafin a kubutar da sauran
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Filato - Dakarun rundunar Operation ENDURING PEACE sun ceto mutane takwas da aka yi garkuwa da su daga dajin Pandam da ke karamar hukumar Qua’an Pan a jihar Filato.
Rundunar ta tabbatar da nasarar aikin ne a ranar Juma’a ta hanyar wata sanarwa da jami’in yada labarai na rundunar, Kyaftin Chinonso Oteh, ya fitar.

Kara karanta wannan
NADCEL: An gano sabuwar hanyar da ake damfarar ƴan Najeriya da sunan rundunar soji

Source: Twitter
Sojoji sun kai farmaki dajin Filato
A cewar sanarwar, an gudanar da aikin ne da misalin karfe 3:00 na daren ranar Laraba, 24 ga watan Yuni, bayan samun sahihan bayanan sirri kan kasancewar wasu masu garkuwa da mutane a cikin dajin, in ji rahoton Punch.
Rundunar ta ce dakarun da aka jibge a garin Namu sun gudanar da wani samame na musamman domin dakile ayyukan masu laifin.
Kyaftin Oteh ya bayyana cewa yayin aikin, sojojin sun yi arangama da wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne, inda aka yi musayar wuta.
Ya ce masu laifin sun rika harbi ba kakkautawa yayin da suke kokarin tserewa daga wajen da sojojin suka kai farmaki. A cewarsa, rikicin da ya barke yayin musayar wutar ya bai wa wasu daga cikin wadanda aka sace damar tserewa.
An kubutar da wadanda aka sace
Sanarwar ta ce:
“Yayin samamen, sojoji sun yi musayar wuta da wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne, wadanda suka rika harbi ba kakkautawa domin su nemi tsira. A wannan yanayi, mutane uku daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su sun samu damar tserewa."

Kara karanta wannan
Yadda matar Janar Rabe ta ki tafiya ta bar shi a daji duk da barazanar 'yan bindiga
Bayan haka, rundunar ta ce ta ci gaba da bincike cikin dajin domin gano sauran wadanda aka yi garkuwa da su, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
A yayin wannan binciken, sojojin sun gano karin mutane biyar da aka sace, wanda ya kawo adadin wadanda aka ceto zuwa takwas.
Rundunar ta ce dukkan wadanda aka ceto suna cikin koshin lafiya kuma ana kokarin hada su da iyalansu.
Rundunar na bin sawun masu laifin

Source: Original
Rundunar Operation ENDURING PEACE ta bayyana cewa har yanzu dakarunta na ci gaba da bin sawun masu garkuwa da mutanen da suka tsere domin kamo su ko dakile ayyukansu.
Ta kuma ce nasarar aikin ya samu yabo daga al’ummomin yankin da abin ya shafa, inda suka yi alkawarin ci gaba da bai wa jami’an tsaro bayanai domin taimakawa wajen kawo karshen laifuka.
Rundunar ta bukaci jama’a su kara hadin kai da jami’an tsaro wajen dakile ayyukan masu aikata laifuka tare da dawo da zaman lafiya a yankunan da take gudanar da aiki.
An gano wurin kera makamai a Filato
A wani labari, mun ruwaito cewa, sojoji sun samu nasarar gano wasu wurare da ake kera makamai a cikin jihar Filato da ke fama da rikicin kabilanci da manoma da makiyaya.
Rahotanni sun bayyana cewa jami'an sun samu nasarar kama mutane biyar tare da ƙwace bindigu da kayan aikin ƙera makamai a kamfanonin.
Sojoji sun ce suna ci gaba da farautar sauran makamai da harsasai da ke hannun miyagun yayin da ake kokarin shawo kan matsalar tsaro a yankin.
Asali: Legit.ng
