CPC: Baraka Ta Kunno kai a Bangaren Buhari kan Goyon bayan Tinubu a 2027
- Tsohon Antoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami, ya ce Tanko Al-Makura ba shi da ikon magana da sunan bangaren CPC a jam’iyyar APC
- Malami SAN ya bayyana cewa shawarwarin da aka yanke na marawa Tinubu baya na wasu mutane ne, ba na 'ya 'yan CPC gaba ɗaya ba
- Ya kuma musanta jita-jitar cewa zai koma jam’iyyar SDP, yana cewa har yanzu yana cikin APC, sai dai yana tattaunawa da wasu kungiyoyi
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kebbi - Tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), ya ce bangaren tsohon gwamnan Nasarawa, Tanko Al-Makura, ba shi da hurumin magana da sunan bangaren CPC da ke cikin APC.
A sanarwar da mai magana da yawunsa, Muhammed Bello Doka ya fitar, Malami ya ce ba kowa ne cikin mutanen da ke kusa da Al-Makura ke da damar yanke hukunci da sunan CPC ba.

Asali: Facebook
Vanguard ta wallafa cewa sanarwar ta biyo bayan wata takarda da wasu tsofaffin ‘yan CPC suka fitar suna goyon bayan Bola Tinubu da shan alwashin cigaba da zama a APC har 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abubakar Malami ya rusa matsayar Al-Makura
Malami ya ce yana da muhimmanci a tantance su wanene ainihin ‘yan bangaren CPC, yana tambaya ko su Al-Makura, Adamu Adamu, Bello Masari da Faruk Adamu Aliyu ne za su wakilci bangaren?
Ya bayyana cewa irin wannan matsaya da suka dauka tamkar neman farfado da tasirinsu ne cikin jam’iyyar APC domin amfanin kansu, ba tare da sahalewar bangaren CPC ba.
Malami ya jaddada cewa CPC ita kadai ce za ta iya fitar da matsayarta, ba wasu mutane da ke daukar kansu matsayin wakilai ba.
Malami zai koma jam'iyyar SDP?
Dangane da rade-radin cewa yana shirin barin APC zuwa jam’iyyar SDP, Malami ya ce hakan ƙage ne maras tushe.
Abubakar Malami ya tabbatar da cewa har yanzu yana cikin APC, sai dai yana tuntubar wasu bangarori daban-daban.
A cewarsa, yana nan cikin harkar siyasa, kuma zai bayyana matsayinsa na gaba a lokacin da ya dace.
Mai magana da yawunsa ya kara da cewa Malami na da cikakken ‘yanci na shiga kowace jam’iyya da kuma tsayawa takara a jihar Kebbi idan bukatar hakan ta taso.

Asali: Facebook
CPC: Matsayar Al-Makura a kan Tinubu
A farkon makon nan ne Tanko Al-Makura da wasu tsofaffin ‘yan CPC suka fitar da sanarwa bayan wata ganawa, suna goyon bayan Bola Tinubu da manufofinsa.
Sai dai Malami ya ce sanarwar ta su ba ta fito da matsayar CPC gaba daya ba. Haka kuma, Buhari ya taba fada wa shugaban APC, Ganduje, cewa kowa na da ‘yancin shiga jam’iyyar da yake so.
Ganduje ya ce Abuja za ta dawo hannun APC
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje ya ce bai kamata a bar birnin tarayya a hannun 'yan adawa ba.
Abdullahi Ganduje ya bayyana haka ne yayin wani taron karbar 'yan jam'iyyun hamayya da suka koma APC a Abuja.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin na cikin manyan 'yan jam'iyyar APC da suka halarci taron.
Asali: Legit.ng