"Kafin Lokaci Ya Kure"; Yaron Gwamna Bala Ya Rubuta Budaddiyar Wasika ga Mahaifinsa

"Kafin Lokaci Ya Kure"; Yaron Gwamna Bala Ya Rubuta Budaddiyar Wasika ga Mahaifinsa

  • Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya samu budaddiyar wasika daga wajen dansa, Shamsudeen Bala Mohammed
  • Shamaudeen Bala Mohammed ya yaba kan irin ayyukan raya kasa da nasararin da Gwamna Bala ya samu cikin shekaru bakwai a kan mulki
  • Sai dai, Shamsudeen ya kuma jawo hankalin Gwamna Bala Mohammed kan abubuwan da ya kamata gwamnatinsa ta mayar da hankali a kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Bauchi - Shamsudenn Bala Mohammed yaron Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi, ya rubuta budaddiyar wasika zuwa ga mahaifinsa.

Shamsudeen Bala Mohammed ya rubuta wasikar ne domin jawo hankalin Gwamna Bala kan halin da ake ciki a Bauchi.

Yaron gwamnan Bauchi ya rubuta wasika ga mahaifinsa
Shamsudeen Bala Mohammed da Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi Hoto: Shamsudeen Bala Mohammed
Source: Facebook

Legit Hausa ta fahimci cewa Shamsudeen Bala Mohammed ya sanya wasikar ne a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis, 25 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya bukaci mutanen Kano su sake zabar Tinubu, ya fadi amfanin hakan

An jawo hankalin Gwamna Bala

Shamsudeen ya bayyana cewa ya rubuta wasikar ne domin bayyana ra'ayinsa cikin girmamawa, tare da nuna damuwa kan halin da ake ciki a Bauchi.

"A cikin shekaru bakwai da suka gabata, mun shaida irin gagarumin ci gaban da gwamnatinka ta kawo. Gine-ginen makarantu, hanyoyi, da asibitoci, duk sun zama shaidar jajircewarka wajen raya jihar Bauchi."
"Duk da haka, yayin da muke tunkarar zaɓen 2027, ina ganin akwai buƙatar jawo hankalin mu akan wani babban koke da ake da shi a tsakanin matasa da al’ummarmu." Ya bayyana cewa ayyukan raya kasa suna da muhimmanci amma akwai abubuwan da suke bukatar daukin gwamnati.
"Gaskiya ne cewa ayyukan raya ƙasa suna da muhimmanci, amma akwai wani giɓi tsakanin waɗannan ayyuka da kuma buƙatun yau da kullum na al’umma."
"Mutane suna cewa, duk da kyawun gine-gine, hakan ba ya magance matsananciyar rayuwa ko kuma rashin biyan kudaden sallamar ma’aikata (gratuity) da suka daɗe suna jira."

Kara karanta wannan

Babbar mota ta burma kan 'yan APC suna tafiya kamfen, an samu asarar rai

- Shamsudeen Bala Mohammed

Matasa na bukatar dauki a Bauchi

Shamsudeen ya bayyana cewa matasa suna cikin wani hali, inda ya ba da shawara ga Gwamna Bala cewa a waiwaye su domin a tallafa masu.

"Matasanmu sun fara kaiwa wani matsayi na ƙunci, kuma su ne ginshiƙan goyon bayan mu. Ba wai roƙon abinci suke yi ba kawai, a’a, suna son su ga an samar musu da hanyoyin dogaro da kai."
"Ina mai ba da shawarar cewa gwamnati ta duba yiwuwar samar da sabon tsari na musamman don tallafawa matasa da mata ta hanyar samar da "seed funding" (jari) don ƙananan sana’o’i, da kuma tsare-tsaren da za su bai wa matasa damar samun aiki a cikin ayyukan da gwamnati take yi."
"Mai Girma, tuni ka kafa tarihi da ayyukan raya ƙasa. Ina roƙon ka da ka sa a mataki na gaba, a mayar da hankali sosai wajen "raya ɗan adam" don matasan Bauchi su ji daɗin wannan gwamnati. Muna fatan ganin an ɗauki matakin da zai kwantar da hankulan al’umma kafin lokaci ya kure."

Kara karanta wannan

"Ba makamin azabatarwa ba ne"; Atiku ya nuna damuwa kan sharuddan belin El Rufai

- Shamsudeen Bala Mohammed

Shamsudeen Bala Mohammed ya ba da shawara ga Gwamna Bala
Shamsudeen Bala Mohammed tare da Gwamna Bala Mohammed Hoto: Shamsudeen Bala Mohammed
Source: Facebook

Batun takarar Gwamna Bala da Jonathan

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yi martani kan batun cewa zai iya takara tare da Goodluck Jonathan a zaben 2027.

Bala Mohammed ya karyata jita-jitar cewa yana cikin shirye-shiryen tsayawa takarar mataimakin shugaban ƙasa tare da Goodluck Jonathan.

Gwamnan ya bayyana cewa manufarsa ita ce neman wakiltar mazabar Bauchi ta Kudu a Majalisar Dattawa ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APM.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng