Da Gaske an Hana Shettima Shiga Aso Villa? Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Bayani
- Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa babu wani lokaci da aka hana Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, shiga Aso Villa
- Gwamnatin tarayya ta bayyana jita-jitar a matsayin karya da ke nufin haddasa rikici tsakanin shugaban kasa da mataimakin nasa
- Fadar shugaban kasa ta bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da labaran karya, su ci gaba da dogaro da kafofin watsa labarai masu inganci
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Fadar shugaban kasa ta karyata jita-jitar da ke yawo a wasu kafafen yanar gizo cewa an hana Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, shiga fadar Aso Villa.
Hadimin shugaban kasa kan yada labarai da sadarwa na ofishin Kashim Shettima, Stanley Nkwocha ya ce batun bai da tushe balle makama.

Asali: Twitter
Legit ta tattaro da bayanan da Stanley Nkwocha ya yi kan lamarin ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar Stanley Nkwocha, manufar irin wadannan rahotanni ita ce tada hankali da kuma jefa fadar shugaban kasa cikin rudani.
Sai dai duk da haka, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na da kwarin guiwar cigaba da gudanar da mulki cikin hadin kai da gaskiya.
Akwai sabani tsakanin Tinubu da Shettima?
Sanarwar ta bayyana cewa babu wani lokacin da aka toshe hanya ko sanya sojoji domin hana mataimakin shugaban kasa shiga ofis.
Fadar shugaban kasa ta ce labaran da ke yawo sun fito ne daga wasu shafukan bogi da ke kokarin tunzura al’umma da yada karya.
Punch ta wallafa cewa sanarwar ta ce:
"Labaran cewa an hana Mataimakin Shugaban Kasa shiga Villa abin dariya ne, kuma wata manuniya ce ta yadda wasu ke amfani da jita-jita don biyan bukatunsu na siyasa,"
Sanarwar ta kara da cewa akwai fahimta mai karfi tsakanin Shugaban Kasa Bola Tinubu da mataimakinsa, kuma duk wani kokari na tada fitina tsakanin su ba zai kai labari ba.

Asali: UGC
An bukaci jama’a su yi watsi da jita-jita
Fadar shugaban kasa ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da goyon bayan gwamnatin Tinubu da Shettima, tare da gujewa yada labaran karya.
An bayyana irin wadannan jita-jita a matsayin kokarin wasu da ke so su ruguza amintakar da ke tsakanin manyan shugabannin kasar.
A cewar sanarwar:
"Shettima bai da lokacin sauraron irin wadannan batutuwa na bogi. Ya fi mayar da hankali wajen taimakawa shugaban kasa don kawo gyara a Najeriya."
A karshe, sanarwar ta gode wa ‘yan Najeriya da ke ci gaba da nuna goyon baya da kuma fatan kafofin yada labarai za su ci gaba da neman sahihan bayanai daga ingantattun majiyoyi.
Atiku ya bukaci Tinubu ya dawo gida
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bukaci a sanya dokar ta baci kqn gwamnatin Bola Tinubu.
Atiku Abubakar ya ce Bola Tinubu ya ki mayar da hankali kan matsalolin Najeriya yayin da ake cigaba da kashe mutane a jihohi dabam-dabam.
Ya kara da cewa ya kamata Bola Tinubu ya bar kasar Faransa da ya ce ya tafi hutun aiki domin dawowa gida ya fuskanci matsalolin Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng