Matawalle Ya Fallasa 'Yan Siyasar Arewa Masu Sukar Tinubu, Ya Fadi Manufarsu
- Ƙaramin ministan tsaro Bello Matawalle ya nuna rashin jin daɗinsa kan sukar da wasu ƴan siyasar Arewacin Najeriya ke yi wa Bola Tinubu
- Bello Matawalle ya bayyana cewa ƴan siyasar da ke hakan, ba suna yi ba ne da zuciya ɗaya sai don wata manufa ta siyasa
- Tsohon gwamnan na jihar Zamfara ya nuna cewa suna sukar Shugaban ƙasan ne domin su yi suna a siyasance ba komai ba
- Ya zarge su da bin wannan hanyar bayan sun gaza samun muƙamai a ƙarƙashin gwamnatin mai girma Bola Tinubu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya caccaki ƴan siyasan Arewa masu sukar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Bello Matawalle ya bayyana cewa wasu ƴan siyasar Arewa da ke sukar Shugaba Bola Tinubu na yin hakan ne kawai don neman samun farin jini a siyasance.

Asali: Twitter
Ƙaramin ministan tsaron ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka na musamman kan harkokin siyasa, Ibrahim Goga, ya fitar a ranar Juma'a, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Matawalle ya ce kan ƴan siyasar Arewa?
Ministan tsaron ya zargi ƴan siyasan da ƙoƙarin ɓata sunan shugaban ƙasan saboda sun kasa samun muƙamai a gwamnatinsa.
Matawalle ya ƙara da cewa wasu fitattun ƴan siyasar Arewa na ɗaukar nauyin yaɗa ƙarya da bayanan da ba su da tushe domin ɓoye gazawarsu a baya da kuma rashin samun muƙamai a cikin gwamnatin tarayya ta yanzu.
“Waɗannan mutanen sun samu dama su yi shugabanci a baya amma ba su yi wani abin a zo a gani ba."
"Yanzu kuwa, suna nuna kansu a matsayin masu kare muradun jama’a, suna amfani da ƙarya da hawayen ƙarya domin su samu tausayin jama’a."
- Bello Matawalle
Haka kuma, ya ƙaryata ikirarin da ke cewa Tinubu barazana ne ga siyasar Arewa, yana mai cewa irin waɗannan maganganu ba su da tushe, kuma ana yin su ne kawai saboda siyasa.
Matawalle ya ba ƴan Arewa shawara

Asali: Facebook
Matawalle ya buƙaci ƴan Arewa da kada su yarda da maganganun raba kawuna, yana mai jaddada muhimmancin haɗin kai da goyon bayan shugaban kasa domin cimma zaman lafiya, ci gaba, da makoma mai ɗorewa ga ƙasar nan.
“Ya kamata mu zama ɓangare na mafita, ba matsala ba. Arewa za ta ci gajiya fiye da yadda ake tunani idan aka zauna cikin haɗin kai tare da goyon bayan shugabanci na gari."
- Bello Matawalle
Matawalle ya caccaki Amaechi
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya caccaki tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi.
Matawalle ya soki Amaechi ne bayan ya yi wasu kalamai masu nuna cewa Shugaba Bola Tinubu ba zai miƙa mulki cikin sauƙi ba.
Ministan ya bayyana cewa kalaman na Amaechi ba su dace ba domin za su iya tunzura jama'a su ɗauki doka a hannunsu.
Matawalle ya gargaɗi tsohon ministan kan yin irin waɗannan kalaman, inda ya nuna cewa wanda aka samu yana haddasa rikici zai fuskanci hukunci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng