Bincike: An Gano Gaskiyar Hoton da Aka ga Kwankwaso Sanye da Hula Mai Tambarin Tinubu

Bincike: An Gano Gaskiyar Hoton da Aka ga Kwankwaso Sanye da Hula Mai Tambarin Tinubu

  • An fara yaɗa hoton Kwankwaso sanye da hula mai tambarin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a kafafen sada zumunta na zamani
  • Hoton ya fara yaɗuwa ne a daidai lokacin da ake jita-jitar cewa jagoran NNPP ɓa kasa, Rabiu Musa Kwankwaso na shirin komawa APC
  • Binciken da aka yi don gano gaskiya ya nuna hoton ƙirkirarre ne, asalin hoton ya nuna Kwankwaso na sanye da jar hular Kwankwasiyya ne

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Wani hoto da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna dan takarar shugaban kasa na NNPP a zaben 2023, Rabiu Kwankwaso, sanye da hula mai tambarin Bola Tinubu.

A hoton wanda aka ɗauka a filin jirgin sama, an ga Kwankwaso sanye da hula mai tambarin nan da ake dangantawa da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

Kwankwaso.
Hoton Kwankwaso sanye da hula mai tambarin Tinubu kirkirarre ne Hoto: @Onsogbu
Asali: Twitter

Masu amfani da kafafen sada zumunta, musamman a X (Twitter) da Facebook, sun yaɗa hoton suna ikirarin cewa Kwankwaso ya bar NNPP ya koma jam’iyyar APC mai mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan ya samo asali ne saboda alamar da ke jikin hular da aka ce Kwankwaso ya sa, wacce alama ce da ta yi ƙaurin suna saboda ana yawan ganinta a hular Shugaba Tinubu.

Yadda hoton Rabiu Kwankwaso ya yaɗu

A ranar Talata, wani mai amfani da X mai suna @Onsogbu, wanda dan jam’iyyar APC ne, ya wallafa hoton da cewa:

“Kwankwasiyya yanzu kuma da hular Tinubu mai tambari. Barka da zuwa gida ranka ya dade. Rayuwa sauƙi gare ta.”

Wannan hoto da ya wallafa ya samu fiye da mutane 30,000 da suka kalla, da wasu 500 da suka nuna sha'awa yayin da wasu akalla 80 suka tura wa abokansu.

A Facebook, wani mai suna Benjamin Ifeanyi Apugo ya wallafa hoton tare da rubuta:

“Duba hular da Kwankwaso ya sa yau. Idan ka san Tinubu sosai, ba za ka raina kwarewarsa a siyasa ba.”

Hoton ya bayyana ne a yayin da ake rade-radin cewa Kwankwaso na shirin ficewa daga NNPP zuwa APC saboda rikicin shugabanci da ke cikin jam’iyyarsa.

Menene gaskiyar wannan hoto?

The CableCheck ta yi amfani da manhajar Google Lens domin tantance hoton, inda ta gano cewa hoton asali an wallafa shi tun a ranar 8 ga Nuwamba, 2022 a shafin jam’iyyar NNPP na Facebook.

An dauki hoton ne a filin jirgin sama na Akanu Ibiam da ke jihar Enugu, lokacin da wasu jiga-jigan jam’iyyar NNPP suka tarbi Kwankwaso.

A hoton na asali, Kwankwaso na sanye da hula ja da aka fi sani da alamar Kwankwasiyya, wadda za a iya kira da tambarinsa na siyasa.

Wannan ya tabbatar da cewa hoton da ke yawo an canza shi ne ta hanyar amfani da fasahar zamani domin sanya tambarin Tinubu a kan hular da Kwankwaso ke sanye da ita.

A shekarar 2024, an wallafa wannan hoton da aka kirkira a Facebook, amma magoya bayan Kwankwaso suka fito suka karyata shi da gaggawa.

Hukunci: Kwankwaso ya sanya hular Tinubu?

Hoton da ya nuna Kwankwaso sanye da hular da ke dauke da tambarin Tinubu ba gaskiya ba ne.

Binciken da aka yi ya tabbatar da cewa hoton ƙirkirarre ne, asalin hular da Kwankwaso ke sanye da ita ja ce amma aka canza ta.

APC ta buɗe ƙofa ga Kwankwaso a Kano

A wani labarin, kun ji cewa shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas ya bayyana cewa ƙofar jam'iyyar a buɗe yake ga Kwankwaso da sauran masu sha'awar shiga.

Abdullahi Abbas ya yi wannan magana ne a wata hira da manema labarai yayin da jita-jita ta ƙara karfi kan batun Kwankwaso na shirin haɗewa da APC.

A cewarsa, jam'iyyar APC ta kowa da kowa ce, don haka duk mai buƙatar shiga ya garzaya mazaɓarsa ya yi rijista.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262