Musulmai na cikin Wani Yanayi da Aka Fara Yunkurin Haramta Kiran Sallah a Denmark

Musulmai na cikin Wani Yanayi da Aka Fara Yunkurin Haramta Kiran Sallah a Denmark

  • Gwamnatin kasar Denmark ta bayyana shirinta na haramta kiran sallah ta lasifa a masallatan da mabiya addinin musulunci ke ibadarsu
  • Ministan harkokin shige da fice na Denmark Morten Bødskov ne ya sanar da hakan, yana mai cewa za a kafa dokar haramcin
  • Ana ganin dai duk wata doka irin wannan za ta fuskanci kalubalen shari'a saboda kundin tsarin mulkin kasar na kare 'yancin addini.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau dankullum

Denmark - Ministan shige da fice na Denmark, Morten Bødskov, ya bayyana cewa gwamnatin kasar na shirin haramta kiran sallah ta amfani da lasifika.

Ministan ya bayyana cewa bai kamata karar kiran sallah da musulmai ke yi akalla sau biyar a kowace rana ya rika tashi a fadin kasar ba.

Musulmai.
Musulmai suna tsakiyar gudanar da Sallah a Masallaci Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Tribune Nigeria ta rahoto cewa ministan, wanda dan jam'iyyar Social Democrats ne, ya ce gwamnati za ta sake bude bincike domin duba yiwuwar samar da tsarin doka da zai ba da damar aiwatar da haramcin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Sakkwato ta yi magana kan rahoton da ake yadawa game da Bello Turji

An fara shirin haramta kiran Sallah

Da yake magana da manema labarai, Bødskov ya ce:

"Bai kamata a rika jin kiran sallah a saman gidajen mutane a Denmark ba. Ba shi da wuri a Denmark, kuma bai kamata 'dan kasar ya rika tunanin tamkar ta shiga wata unguwar Islamabad ba."

A halin yanzu dai wasu yankuna na Denmark, ciki har da babban birnin Copenhagen, sun riga sun takaita amfani da lasifika wajen kiran sallah saboda dokokin hayaniya na kananan hukumomi.

Musulunci na kara yaduwa a Denmark

Ministan ya kuma bayyana cewa karuwar tasiri da yaduwar addinin Musulunci a kasar na kara mamaye jama'a fiye da yadda ya kamata, kamar yadda The Telegraph ta ruwaito.

Kiran sallah, wanda ake kira Adhan, ana yin sa sau biyar a rana domin gayyatar Musulmi zuwa ibada, kuma a al'ada ana amfani da lasifika da aka kafa a kan hasumiyar masallaci don mutane su ji.

Wannan shi ne karo na uku da wani ministan shige da fice daga jam'iyyar Social Democrats ke kokarin samar da doka domin haramta kiran sallah ta lasifika, bayan irin wannan yunkuri da aka yi a 2020 da 2025.

Kara karanta wannan

Bello Turji ya ba Najeriya zabin yaki ko zaman lafiya a sabon bidiyo

Ana sa ran za a kalubalanci dokar

Ana sa ran duk wani yunkurin haramta kiran sallah zai fuskanci bincike da kalubalen shari'a, domin kundin tsarin mulkin Denmark ya bai wa mutane damar gudanar da ibadarsu a bainar jama'a.

Sai dai dokokin kasar suna ba gwamnati damar sanya wasu takunkumai a wasu lokuta na musamman, ciki har da hana wa'azin da ake ganin yana barazana ga tsarin dimokuradiyya ko kuma goyon bayan kungiyoyin da aka haramta.

Denmark
Ministan harkokin shige fa fice na kasar Denmark, Morten Bødskov Hoto: Emil Nicolai
Source: Getty Images

Kasar Denmark na da yawan jama'a kusan miliyan shida, ciki akwai muusulmai kimanin 270,000.

Haka kuma akwai kusan masallatai 100 a kasar, ciki har da Grand Mosque of Copenhagen, wanda bisa yarjejeniya da hukumomin yankin ba ya amfani da lasifika wajen kiran sallah.

Adadin musulmin da suka je hajjin 2026

A wani rahiton, kun ji cewa hukumar ƙididdiga ta Saudiyya ta sanar da cewa mahajjata miliyan 1.7 ne suka gudanar da aikin Hajjin 2026, adadin da ya zarce na 2025.

Kara karanta wannan

Mutane sun kama malamar Islamiyya da karfi sun kona ta, 'yan sanda sun magantu

Hukumar ta bayyana cewa kididdigar ta ƙunshi dukkan maza da mata da suka halarci aikin Hajjin bana a birnin Makkah da sauran wurare masu tsarki.

Aikin Hajji na ɗaya daga cikin rukunnan Musulunci guda biyar kuma wajibi ne ga duk musulmin da yake da hali da lafiya ya yi shi sau ɗaya a rayuwarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262