Minista Ya Rutsa Shugaban Jami’a kan Zargin Nada Hadimai 24 a Ofishinsa

Minista Ya Rutsa Shugaban Jami’a kan Zargin Nada Hadimai 24 a Ofishinsa

  • Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ya aika wa sabon shugaban jami’a tambaya kan nadin mataimaka 24 da ake zargin ya yi
  • A cikin wasikar ma’aikatar ilimi, an umarci shugaban jami’ar da ya soke nadin nan take tare da gabatar da hujjar cikin gaggawa
  • Ma’aikatar ta gayyaci shugaban jami’ar zuwa Abuja ranar 29 ga Yunin 2026 domin tattauna batun shugabanci, bin doka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ikeja, Lagos - Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ya bukaci karin haske game da zargi kan sabon shugaban Jami'ar Tarayya ta fasaha da ke Owerri.

Ma'aikatar ilimi ta nemi bahasin daga Ikechukwu Dozie, kan nadin hadimai 24 da aka yi a ofishinsa, wanda ma’aikatar ta ce akwai alamun rashin bin ka’idoji.

Minista ya taso shugaban jami'a a gaba kan zargin nada hadimai 24
Ministan ilimi a Najeriya, Tunji Alausa. Hoto: Federal Ministry of Education.
Source: Facebook

Hakan wata takarda mai dauke da kwanan watan 25 ga Yuni, 2026, wadda mukaddashin daraktan ilimin jami’o’i, Kareem O.L., ya sanya wa hannu, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya kawo hanyar magance rikicin manoma da makiyaya

Ma'aikatar ilimi ta soki shugaban jami'a

Sanarwar ta bayyana nadin a matsayin wanda bai dace da dokoki da tsarin jami’o’in tarayya ba.

Takardar ta ce hankalin ministan ya karkata ne zuwa wata sanarwa da jami’ar ta fitar ranar 22 ga Yuni, 2026, wadda ta kunshi nadin mutane 24 a mukamai daban-daban a ofishin shugaban jami’ar.

Ma’aikatar ta bayyana cewa bayan nazarin takardar cikin gida da jami’ar ta fitar, ta gano cewa nadin ya sabawa dokoki da tsare-tsaren da ke jagorantar daukar ma’aikata da gudanar da ayyuka a jami’o’in tarayya.

Ana zargin shugaban jami'a da nada hadimai 24
Taswirar jihar Imo da jami'ar da ake tuhumar shugabanta ta fito. Hoto: Legit.
Source: Original

Umarnin da aka ba shugaban jami'ar

Saboda haka, an umarci shugaban jami’ar da ya soke dukkan nadin nan take tare da gabatar da hujjojin da ke nuna ya bi wannan umarni ba tare da bata lokaci ba.

Har ila yau, an aika kwafin wasikar zuwa Hukumar kula da jami'o'in Najeriya domin sanar da ita halin da ake ciki da kuma matakin da ma’aikatar ta dauka.

Kara karanta wannan

Wata 'yar sanda ta jefa kanta a shari'ar N300m a Abuja, kotu ta sa a kamo ta

Ma’aikatar ilimi ta kuma gayyaci shugaban jami’ar zuwa hedikwatarta ranar Litinin, 29 ga Yuni, 2026, domin karin tattaunawa kan wannan batu da sauran al’amuran shugabanci da rikon amana a jami’a.

A cewar takardar, za a tattauna batutuwan da suka shafi bin ka’idoji, gaskiya, rikon amana da kuma tabbatar da cewa ana gudanar da jami’o’in tarayya bisa tsarin da doka ta tanada, cewar Punch.

Gwamnatin tarayya ta hana amfani da Dr

Mun ba ku rahoto a baya cewa gwamnatin tarayya ta hana masu digirin girmamawa amfani da Dr a jikin sunayensu bayan gano cewa ana karya ka'ida a tsarin.

Ministan ilimi na tarayya, Dr. Tunji Alausa ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da manema labarai a fadar shugaban kasa.

Alausa ya ce duk jami’ar da ta saba wa wannan umarni za ta fuskanci hukunci, yana mai cewa an umurci shugabannin jami’o’i su daidaita tsarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.