Jigon PDP Ya Karaya, Ya Fadi yawan Jihohi da Tinubu Zai Lashe a Zaben 2027
- Jigo a jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ya yi hasashe game da jihohin da Bola Tinubu zai ci a zaben 2027 da ake tunkara
- Segun Sowunmi ya ce fafatawar 2027 ta fara bayyana a matsayin gwabza tsakanin Tinubu da Atiku Abubakar da ke ADC
- Ya bayyana cewa Tinubu na iya samun karin kuri’u a Kudu maso Gabas, Kudu maso Kudu, Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Wani jigo a jam’iyyar PDP, Segun Sowunmi, ya yi hasashen cewa Bola Ahmed Tinubu zai lashe jihohi da yawa.
Sowunmi ya ce Tinubu na iya samun nasara a jihohi kusan 22 a zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

Source: Facebook
Jigon PDP ya bayyana haka ne yayin da ya ke magana a gidan talabijin na Arise a ranar Alhamis 25 ga watan Yunin 2026.
Jigon PDP ya yi hasashen zaben 2027
Sowunmi ya ce alamun siyasa na nuna cewa fafatawar shugaban kasa ta 2027 za ta kasance tsakanin Tinubu da Atiku Abubakar.
Ya ce:
“Zaben tsakanin Tinubu da Atiku ne kawai, babu wata shakka a kan hakan.”
Duk da kasancewarsa mamba a jam’iyyar adawa ta PDP, Sowunmi ya ce sauye-sauyen siyasa da ake gani yanzu na iya taimakawa Tinubu wajen inganta sakamakonsa.
Ya bayyana cewa shugaban kasar na iya samun kuri’u masu yawa a Kudu maso Gabas, yankin da jam’iyyar APC ba ta saba samun karfin kuri’a ba.
Sowunmi ya ce Tinubu zai samu kyakkyawan sakamako a Kudu maso Yamma, sannan yana ganin Kudu maso Kudu ma na iya ba shi karin kuri’u.
Ya kuma bayyana cewa shugaban kasar zai yi matukar kyau a Arewa ta Tsakiya, sannan zai fi yadda ya yi a zaben baya a Arewa maso Yamma.

Source: UGC
Jihohin da ake hasashen Tinubu zai lashe
A cewarsa, watakila nasarorin ba za su kasance masu tazara sosai ba, amma idan ya yi aiki tukuru, zai iya lashe jihohi kusan 22.
Game da Arewa maso Yamma, Sowunmi ya ce ya kamata a duba tasirin manyan ’yan siyasa da masu ruwa da tsaki da ke da karfi wajen tafiyar da siyasa.
Ya ba da misalin Kano, inda ya ce akwai manyan ’yan siyasa da masu arziki da ke taka muhimmiyar rawa wajen tsara yanayin siyasa wanda ke da muhimmanci.
Jigon na PDP ya ce hasashensa ya samo asali ne daga yadda gwamnoni da fitattun ’yan siyasa ke sauya matsaa da kulla alaka kafin zaben 2027.
Jigon PDP ya magantu kan zaben 2027
Mun ba ku labarin cewa wani jigo a jam'iyyar PDP, Segun Sowunmi, ya yi magana kan zaben shugaban kasa na shekarar 2027.
Tsohon dan takarar gwamnan na jihar Ogun ya bayyana cewa jam'iyyar ADC ba za ta kai labari ba a zaben da ake tunkara.
Ya nuna cewa zaben zai kasance ne a tsakanin jam'iyyar APC mai mulki da babbar mai adawa a Najeriya watau PDP.
Asali: Legit.ng