Kotun Ta Yi Hukunci a Shari'ar Neman Soke Rijistar ADC da Wasu Jam'iyyun Adawa

Kotun Ta Yi Hukunci a Shari'ar Neman Soke Rijistar ADC da Wasu Jam'iyyun Adawa

  • Jam’iyyar ADC, Accord da wasu jam’iyyu uku sun samu sauƙi bayan Kotun Daukaka Kara ta Abuja ta yi zama kan shari'arsu
  • Lauyan Accord, Musibau Adetunbi, ya ce an samu takardun shari’ar ne a makon nan, saboda haka ya nemi lokaci domin musayar hujjoji
  • INEC ta dage cewa jam’iyyun sun cika sharuddan doka kuma sun lashe kujeru a zabuka, yayin da kotu ta ci gaba da dakatar da soke rajistarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta yi zama kan shari'ar neman soke rijistar wasu jam'iyyun adawa.

Kotun ta dage sauraron ƙarar da ke kalubalantar soke rajistar jam’iyyar ADC, Accord da wasu jam’iyyu uku zuwa ranar 7 ga Yulin 2026.

Kotu ta dage zaman shari'ar da ake yi kan ADC, sauran jam'iyyun adawa
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da sauran jiga-jigan ADC yayin taro a Abuja. Hoto: Atiku Abubakar.
Source: Twitter

Kotu ta sauya ranar shari'ar ADC, jam'iyyun adawa

Kara karanta wannan

Wata 'yar sanda ta jefa kanta a shari'ar N300m a Abuja, kotu ta sa a kamo ta

Kotun ta sauya ranar sauraron shari’ar daga 25 ga Yuni domin bai wa bangarorin da ke cikin ƙarar damar gabatar da takardunsu da musayar hujjoji, cewar Punch.

A zaman kotun na ranar Alhamis, lauyan Accord, Musibau Adetunbi (SAN), ya shaida wa kwamitin alkalai uku karkashin jagorancin Mai Shari’a Abubakar Mohammed cewa an samu kundin shari’ar ne.

Babban lauyan ya bukaci a ba da ɗan lokaci domin bangarorin su gabatar da takardu da kuma musayar bayanan da za su yi amfani da su.

Sauran bangarorin da ke cikin shari’ar ba su yi adawa da bukatar ba, lamarin da ya sa kotun ta dage sauraron ƙarar zuwa rana a ranar 7 ga Yulin 2026.

Ko da yake Adetunbi ya nemi kwanaki uku kacal domin kammala musayar takardu, Mai Shari’a Mohammed ya bayyana cewa wasu alkalai za su kasance wajen Abuja.

Wannan ƙara ta samo asali ne daga hukuncin Mai Shari’a Peter Lifu na Babbar Kotun Tarayya da ya umarci INEC ta soke rajistar jam'iyyar ADC da wasu jam’iyyu hudu.

ADC da wasu jam'iyyun adawa sun samu sauki a shari'ar da ake yi
Harabar babbar kotun tarayya da ke Abuja. Hoto: Light Oriye Tamunotonye / AFP.
Source: Getty Images

Zargin da ake yi kan ADC, jam'iyyun adawa

Kara karanta wannan

Jerin kujerun da APC ta lashe a zaben ranar 20 Yunin 2026

Mai Shari’a Lifu ya yanke cewa jam’iyyun ba su cika sharuddan kundin tsarin mulki da ake bukata domin ci gaba da kasancewa cikin tsarin siyasa ba.

Sai dai INEC ta yi adawa da soke rajistar, tana mai cewa jam’iyyun sun cika sharuddan doka kuma sun samu nasarori a zabukan da suka gabata.

Hukumar zaben ta gabatar da takardun shaidar cin zabe da aka bai wa ‘yan takarar da suka yi nasara karkashin wadannan jam’iyyu a fadin kasa, TheCable ta tattaro.

A ranar 16 ga Yunin 2026, Kotun Daukaka Kara ta ba da umarnin dakatar da aiwatar da hukuncin Babbar Kotun Tarayya har sai an kammala sauraron daukaka karar.

Amaechi: ADC ta fitar da mataimakin Atiku

Kun ji cewa zaben dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam'iyyar ADC na neman kawo sabani tsakanin bangarorin da dama.

Sakataren yada labarai na ADC, Bolaji Abdullahi, ya fito ya yi magana kan batun ko akwai sabani dangane da nadin da aka yi wa Rotimi Amaechi.

Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa jam'iyya ce ke da hakkin fitowa ta sanar da dan takararta kuma sai ta yi shawara kafin ta yi hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.