Wata Sabuwa: Gwamnatin Tinubu Ta Kafa Kwamiti, za a Rage Shigo da Abinci daga Waje

Wata Sabuwa: Gwamnatin Tinubu Ta Kafa Kwamiti, za a Rage Shigo da Abinci daga Waje

  • Gwamnatin tarayya ta kafa kwamiti don dakile dogaro da kayayyakin waje tare da tabbatar da tsaron abinci da makamashi a Najeriya
  • Kashim Shettima ya ce kwamitin zai taimaka waje rage shigo da kayayyaki da kashi 50 , tare da gina tattalin arziki bisa turbar fasaha
  • Kwamitin zai maida hankali kan noma, lafiya, masana’antu, makamashi da albarkatu don samar da canjin rayuwa ga al'ummar kasa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da wani kwamiti na hadin gwiwar ma'aikatun gwamnati domin rage dogaron Najeriya da kayayyakin kasashen waje.

An ce wannan kwamitin zai gudanar da bincike cikin fasaha domin samar da dabarun tabbatar da dorewar tsaron abinci da makamashi a Najeriya.

Kashim Shettima ya kaddamar da kwamitin da zai rage shigo da kayayyaki daga waje
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima (Hagu) tare 'yan kwamitin rage shigo da kayayyaki (Dama) a Abuja. Hoto: @officialSKSM
Asali: Twitter

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ne ya kaddamar da kwamitin a fadar shugaban kasa da ke Abuja, kamar yadda ya sanar a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati ta kafa kwamiti kan shigo da kayayyaki

Kashim Shettima, ya bukaci 'yan kwamitin da su mayar da hankali wajen ganin an rage kudin shigo da kaya daga waje da kashi 50.

Shettima ya bayyana cewa kafa kwamitin na cikin shirin Shugaba Bola Tinubu na samar da wani katafaren dandalin kirkire-kirkire da zai jagoranci tattalin arzikin Najeriya a turbar fasaha.

A cewarsa, burin gwamnatin Tinubu shi ne ta gina tattalin arzikin Najeriya da zai kai darajar dala tiriliyan guda cikin shekaru goma masu zuwa.

"Ba wai mun taru don farfado da gina wannan kwamiti ba ne kawai, sai dai don mu dasa tubalin burin gina Najeriya mai dogaro da kirkire-kirkire, har ta kai mu ga samar da tattalin arzikin da darajarsa ta kai dala tiriliyan guda a cikin shekaru 10. Makomar da muke fata ba za ta kawo kanta ba, dole mu ne za mu gina ta."

- Shettima.

Ayyukan da kwamitin gwamnatin zai gudanar

Dangane da aikace-aikacen kwamitin, Shettima ya ce za su mayar da hankali kan sassa guda biyar masu tasiri wajen sauya rayuwar jama’a.

Ya lissafo su kamar haka:

"Noma da juriya kan sauyin yanayi, inda bincike da kirkire-kirkire za su taimaka wajen samar da abinci ga al’umma da kuma kare muhallinmu.
"Sauran sassan sun hada da inganta masana’antu don daina dogaro da kayayyakin waje; kirkire-kirkire a fannin lafiya don daina shigo da magunguna.
"Haka kuma, amfani da albarkatun kasa ta hanya mai amfani, maimakon fitar da su haka kawai; da kuma tabbatar da wutar lantarki don karfafa tattalin arziki da kare makomar kasar.”

Manufar gwamnati na rage shigo da abinci

Shettima ya kaddamar da kwamitin karfafa tattalin arziki da rage shigo da kayayyaki
Kashim Shettima (na 11 daga hannun Dama) tare da sabon kwamitin da ya kaddamar a Abuja. Hoto: @officialSKSM
Asali: Twitter

Shettima ya bayyana cewa babban burin kafa kwamitin shi ne rage shigo da abinci daga waje da kashi 50, yana mai jaddada cewa “za mu bi diddigin aiyuka, ba iya lissafi kawai ba.”

Mataimakin shugaban kasar ya jero tambayoyi kan haka:

“Ba za mu gamsu da bayanan cikin na'urori kawai ba, muna son yin abin da zai canja rayuwar al’umma. Me zai taimaka wajen rage kudin shigo da abinci da kashi 50?
"Ta yaya za mu ninka yawan magungunan da ake samarwa a cikin gida?
"Mu hada dokoki, bincike da saka jari domin cimma wadannan abubuwa."

Sanata Shettima ya kara da cewa wannan kwamiti mataki ne na farko gabanin taron koli na shugaban kasa kan kirkire-kirkire da Tinubu ya amince da shi.

An cire harajin shigo da abinci daga waje

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta fara ɗaukar matakai don rage tsadar kayan abinci da suka yi tashin gwauron zabo a kasuwannin cikin gida.

Ministan noma da samar da abinci, Sanata Abubakar Kyari, ya bayyana cewa gwamnati ta dakatar da harajin wasu muhimman abinci na wani lokaci.

A cewarsa, an soke haraji kan abinci kamar su shinkafa, masara, wake da alkama na tsawon kwanaki 150 domin saukaka wa talakawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.