Gwamnonin PDP 4 da Ake Tunanin Za Su Koma APC domin Goyon bayan Tinubu a 2027

Gwamnonin PDP 4 da Ake Tunanin Za Su Koma APC domin Goyon bayan Tinubu a 2027

  • A kalla gwamnoni uku na PDP na shirin sauya sheka zuwa APC, domin marawa shugaba Tinubu baya a yunkurinsa na zarce a 2027
  • Gwamna Umo Eno ya bayyana cewa babu jam'iyya a Akwa Ibom yanzu, suna aiki tare da APC domin hadin kai da ci gaban kasa
  • Gwamna Oborevwori, Mbah da Fubara suna nazarin marawa Tinubu baya ba tare da sauya sheka ba, yayin da wasu ke tattaunawa kan sauyin jam’iyya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - A kalla gwamnoni uku zuwa hudu na jam’iyyar PDP na shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Ana zargin gwamnonin sun ɗauki wannan mataki domin marawa Shugaba Tinubu a kokarinsa na tazarce a 2027.

Ana zargin gwamnonin PDP 4 za su koma APC
Majiyoyi sun ce gwamnoni 4 na PDP sun shirya dawowa APC. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Pastor Umo Eno.
Asali: Facebook

Wannan ya biyo bayan rudanin siyasa a wasu jihohin Arewa da ke barazanar janye goyon bayansu ga Shugaban kasa a zaben 2027, cewar Arise TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnonin PDP da ke shirin shiga APC

Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya tabbatar da goyon bayansa ga Tinubu, yana cewa jam’iyyun PDP da APC sun zama jam’iyyar hadin kai.

Amma Gwamna Sheriff Oborevwori na Delta, Peter Mbah na Enugu da Gwamna Fubara na Ribas sun fara nazarin marawa Tinubu baya daga cikin PDP.

Bayan Gwamna Eno ya nuna goyon baya, rahotanni sun ce PDP a jiharsa za ta goyi bayan Tinubu da dawo da Akpabio a matsayin Shugaban Majalisa.

Gwamna Eno ya amince da sauya sheka zuwa APC domin tsoron rashin samun wa’adin tazarce, kuma yana son kare muradinsa tun kafin 2027.

An ce Akpabio ne ke jagorantar tattaunawar sauya sheka, domin kare tsohon gwamna Udom Emmanuel daga binciken EFCC da ke kansa yanzu.

Don nuna godiya ga Eno, Godswill Akpabio ya sha alwashin goyon bayansa a wa’adin tazarce, ta bakin shugaban kwamitin majalisa, Saviour Enyiekere.

Abin da Gwamna Oborevwori ke jira

An ce Oborevwori na Delta na duba ko ya cigaba da kasancewa a PDP yana mara wa Tinubu baya ko kuma ya fita daga jam’iyyar baki daya.

Yana jiran bangare daya ya cika alkawarinsu kafin ya amince da yarjejeniyar da za ta bashi damar tsayawa wa’adin tazarce, Punch ta ruwaito.

Gwamnonin PDP 4 da ake hasashen za su koma APC
Rahotanni sun tabbatar da cewa akwai gwamnonin PDP 4 da ke shirin dawowa APC. Hoto: Nyesom Ezenwo Wike, Sir Siminalayi Fubara.
Asali: Facebook

Shiga APC: Mahangar Fubara da Gwamna Mbah

Gwamna Fubara ma yana duba yiwuwar marawa Tinubu baya, ko ya cigaba da kasancewa a PDP ko kuma ya koma jam’iyyar APC.

Bugu da kari, matsin lamba daga tsohon ubangidansa, Ministan Abuja, Nyesom Wike, wanda ke da karfi a APC ya hana sauya shekar.

Fubara yana ganin cewa zuwa APC zai kare shi daga kokarin da ake yi na hambarar da shi daga kujerarsa ko hana shi sake tsayawa.

A nasa bangaren, Gwamna Mbah, wanda ake ganin yana da alaka da fadar shugaban kasa, na nazarin yiwuwar komawa APC ko cigaba da zama a PDP.

Yana kokarin tabbatar da goyon bayan Tinubu a zaben 2027, tare da kokarin ganin ya samu damar sake tsayawa takara karo na biyu.

2027: Ana zargin haɗa Atiku da Obi takara

Kun ji cewa ana hasashen Atiku Abubakar na shirin takara a 2027 da Peter Obi a matsayin mataimakinsa, domin kalubalantar Bola Tinubu.

Amfanin hadin gwiwar shi ne amfani da karfin Atiku a Arewa da kuma farin jinin Obi a Kudu domin gina babbar jam'iyya adawa.

An ce Atiku zai yi wa'adin shekara hudu kawai, daga 2027 zuwa 2031, sannan ya mika mulki ga Obi wanda zai yi wa'adi biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.