Matawalle Ya Karyata Masu Adawa da APC, Ya Fadi Yadda Tinubu Ya Zamo Kadara ga Arewa
- Karamin Ministan tsaro na ƙasa, Dr. Bello Matawalle, ya musanta rade-radin da ke yawo cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu barazana ne ga Arewa
- A cewarsa, ba a yada irin nasarorin da gwamnatin Tinubu ke samu a fannin tsaro da ci gaban tattalin arziki a shigar
- Matawalle, ya zargi wasu 'yan siyasa a yankin da yada labarai na son zuciya saboda sun rasa wasu abubuwa a gwamnatin Bola Tinubu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Karamin Ministan tsaro, Dr. Bello Matawalle, ya karyata jita-jitar da ke cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu barazana ce ga siyasar Arewacin Najeriya.
A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin siyasa, Ibrahim Goga, ya fitar a ranar Juma’a, Matawalle ya bayyana cewa irin waɗannan furuci ba su da tushe.

Asali: Facebook
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa tsohon gwamnan Zamfara ya bayyana Tinubu a matsayin kadara, kuma mai amfani ga Arewa da ƙasa baki ɗaya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce akwai tabbacin hakan a irin ayyuka da nasarorin gwamnatinsa a fannin tsaro, ayyukan more rayuwa da haɗin kan ƙasa.
Matawalle ya fadi amfanin Tinubu ga Arewa
Nigerian Tribune ta wallafa cewa Matawalle ya ce shugaba Tinubu ya nuna aniyarsa wajen shawo kan ƙalubalen da ke addabar yankin Arewa ta fuskoki da dama.
A cewarsa:
“Wadanda ke amfani da ƙarya da yaɗa jita-jita suna ƙoƙarin neman su yi suna ne, bayan sun gaza samun mafita ta siyasa a rayuwarsu.”
“Jami’an tsaronmu, tare da shawarwarin gaggawa na shugaban kasa, sun samu gagarumar nasara.”
“Lokutan azumin Ramadan da na Easter sun kasance cikin mafi kwanciyar hankali a wasu sassan Arewa a cikin shekaru.”
Matawalle ya caccaki masu sukar Tinubu
Ministan ya zargi wasu ‘yan siyasa da shirya yaɗa ƙarya da nufin ɓoye gazawar su a baya da kuma rashin samun muƙamai a gwamnatin Tinubu.
Ministan ya jaddada cewa ana ci gaba da aikin manyan titunan tarayya da suka hada da na Zariya-Gusau-Talata Mafara-Sokoto da kuma babban titin Abuja-Kaduna-Kano.

Asali: Facebook
A cewar Matawalle:
“Wadannan ayyuka an bar su na shekaru ba tare da an kammala su ba, amma shugaba Tinubu ya dawo da su. Masu suka suna kauce wa ambaton nasarorin nan saboda ba su dace da labarinsu ba.”
Matawalle: An taso Minisan Tinubu a gaba
A baya, kun samu labarin cewa wani jigo a APC reshen Ribas, Eze Chukwuemeka Eze, ya bayyana rashin jin daɗin kalaman Bello Matawalle, da ya yi wa Rotimi Amaechi.
Eze ya soki gargaɗin da Matawalle ya yi kan Amaechi, yana mai cewa hakan bai dace ba, kuma ya kamata ministan ya fi mai da hankali kan ƙalubalen tsaro da ke addabar ƙasar nan.
Ya ce yanzu, lokaci ne da ake buƙatar shugabanni su haɗa kai wajen magance matsalolin da ke damun Najeriya, musamman hare-haren 'yan bindiga, garkuwa da mutane da sauransu.
Asali: Legit.ng