Jihar Borno
Ministan Tsaro Christopher Musa ya ce faɗin dajin Sambisa na ƙara wahalar da ayyukan ceto, yana mai cewa yankin yana da girman da ya kai Belgium.
Kwamishinan Borno, Sainna Buba, ya fito ya janye wata magana mai cike da cece-kuce, tare da neman afuwar jama’a da magoya bayan jam’iyyun adawa a jihar.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya dakatar tare da korar dagatai da masu unguwanni a Malam Fatori saboda rashin zama a yankin.
Kwamishinan Matasa da Wasanni na Borno, Sainna Buba, ya janyo cece-kuce bayan yin barazanar cutar da masu adawa da APC da kuma hana su amfana ta gwamnati.
Gwamna Zulum ya bai wa ɗalibai 30 da suka haddace Alƙur’ani Naira miliyan ɗaya kowanne, tare da bai wa malamai takwas Naira miliyan biyu kowanne.
Dakarun sojojin Najeriya sun dakile harin ‘yan ta’adda a Kukawa, Borno, inda aka kashe mayaka 26 tare da jikkata sojoji huɗu yayin artabu da maharan.
An tabbatar da rasuwar tsohon dan majalisar dattawan Najeriya, Sanata Kaka Mallak Yale a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri da ke jihar Bono ranar Juma'a.
Kungiyar goyon bayan Bola Tinubu ta yi barazanar janye tallafi idan Ali Modu Sheriff ya ci gaba da kasancewa cikin tsarin yakin neman zaben APC na 2027.
Dakarun sojojin Najeriya sun cafke wani mutum da ake zargi da alaka da ISWAP a jihar Borno bayan gano hotonsa tare da wasu dauke da bindigogin AK-47.
Jihar Borno
Samu kari