Sheikh Bala Lau Ya Yi Magana kan Shugaban Izala da 'Yan Bindiga Suka Kashe
- Kungiyar Izala da Sheikh Abdullahi Bala Lau ke jagoranta ta tabbatar da cewa 'yan ta'adda sun kashe daga daga cikin shugabanninta a Kebbi
- Sheikh Abdullahi Bala Lau ya bayyana cewa shugaban Izala na karamar hukumar Besse, Malam Yahaya Balli ya rasu a hannun masu garkuwa
- Shugaban Izala na kasa ya yi kira ga limamai da su dukufa da yin addu'a domin rokon Allah ya kawo karshen matsalolin tsaro da ake fama da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kebbi - Kungiyar Izala ta kasa ta yi magana bayan samun labarin cewa wani daga cikin jagororinta ya rasu a hannun masu garkuwa da mutane a Kebbi.
Tun a kwanakin baya ne 'yan bindiga suka saki bidiyon wasu dattawa biyu suna rokon jama'a da su cece su, inda daga baya aka gano dayan shugaban APC ne, dayan kuma shugaba a Izala.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanin da Sheikh Abdullahi Bala Lau ya yi ne a wani sako da shafin Jibwis Nigeria ya walllafa a Facebook game da mutuwar Malam Yahaya Balli.
Bayanin shugaban Izala, Abdullahi Bala Lau
Kungiyar Izala ta sanar da cewa Sheikh Bala Lau yana mika sakon ta'aziyya ga iyalan Malam Yahaya Balli da 'yan bindiga suka kashe.
Sanarwar Jibwis ta ce:
"Shugaban JIBWIS na tarayyar Najeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau, tare da yan kwamitin zartaswa, na miƙa saƙon ta'aziyya ga iyalan Malam Yahaya Balli, da al'ummar garin Besse da ɗaukacin al'ummar JIBWIS na jihar Kebbi,..
"Bisa rasuwar shugaban JIBWIS na garin Besse, wanda Allah ya yi wa rasuwa a hannun masu garkuwa da mutane."
Izala ta ce marigayin ya rasu ne bayan da wasu 'yan ta'adda suka yi garkuwa da shi, inda Allah maɗaukakin sarki ya karɓi rayuwarsa a hannunsu.
Sanarwar ta kara da cewa:
"Wannan babban rashi ne ba ga iyalansa kaɗai ba, ko ga al'ummar Besse, rashi ne wanda ya shafi ƙasa baki daya."

Source: Facebook
Kiran Sheikh Bala Lau ga limamai
A yayin miƙa sakon, ta'aziyyar, shugaban ya yi kira ga dukkan limamai da su dukufa wurin addu'ar samun mafita daga bala'in rashin tsaro.
Haka kuma yayi kira ga jami'an tsaro da su ƙara kaimi, himma da jajircewa wajen ci gaba da gudanar da ayyukansu na kare rayuka da dukiyoyin al'umma.
A karshe, Bala Lau ya buƙaci gwamnati da masu ruwa da tsaki su ƙara tallafa wa jami'an tsaro domin ƙarfafa yaƙi da ayyukan ta'addanci da sauran laifuffukan da ke barazana ga zaman lafiya.
Babban malamin Izala ya rasu a Bauchi
A wani labarin, kun ji cewa kungiyar Izala a jihar Bauchi ta sanar da rasuwar babban malaminta, Sheikh Dawud Muhammad a ranar Talata.
Shugaban Sunnah TV, Dr Ibrahim Disina ya bayyana cewa marigayin ya shafe shekaru yana yi wa addinin Musulunci hidima a Bauchi da kasa baki daya.
Sauran malamai da suka hada da Sheikh Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo da Dr Ibrahim Jalo Jalingo sun yi ta'aziyyar rasuwar malamin.
Asali: Legit.ng

