'Nigeria Air': EFCC Ta Tona Yadda Ministan Buhari Ya Yaudari 'Yan Kasa da Jirgin Aro

'Nigeria Air': EFCC Ta Tona Yadda Ministan Buhari Ya Yaudari 'Yan Kasa da Jirgin Aro

  • Shaidan hukumar EFCC ya shaida wa kotu yadda tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama ya aro jirgin 'Ethiopian Airlines' a matsayin 'Nigeria Air'
  • Shaidan ya bayyana cewa an yi wa jirgin kwalliyar ƙasar nan, kuma an aro shi na tsawon kwanaki uku kacal a wancan lokaci a shekarar 2023
  • Ya ce an shirya nuna jirgin ne kwanaki kaɗan kafin gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta sauka daga mulkin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Shaida na 12 da hukumar EFCC ta gabatar a kotu, Christopher Odofin, ya shaida wa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Laraba 10 ga watan Yuni, 2026 yadda aka aro 'Nigeria Air.'

Christopher Odofin ya bayyana cewa tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Abubakar Sirika, ya yi amfani da wani jirgin Ethiopian Airlines wajen nuna kamar an ƙaddamar da kamfanin jiragen sama na 'Nigeria Air.'

Kara karanta wannan

Rikicin NDC: Abin da Kwankwaso da Seriake Dickson suka tattauna a zaman Abuja

An kara samun shaidu kan zargin da ake yi wa Hadi Sirika
Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika da ofishin hukumar EFCC a gefensa Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Source: Facebook

EFCC ta wallafa a shafinta na Facebook cewa Odofin ya bayyana hakan ne yayin shari’ar da ake yi wa Sirika kan zargin cin zarafin ofis da kuma karkatar da kuɗin gwamnati da suka haura N2bn.

EFCC: 'Hadi Sirika ya aro jirgin Ethiopia '

A cewarsa, jirgin da aka yi wa ado da tambarin Nigeria Air ya sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja a ranar 27 ga Mayu, 2023, kwanaki uku kafin ƙarshen mulkin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Shaidan ya karanta wani ɓangare na yarjejeniyar da aka ƙulla da Ethiopian Airlines inda aka ce:

“Jirgin zai tashi daga Addis Ababa da yammacin ranar 26 ga Mayu, 2023 domin ya isa Abuja da safiyar 27 ga Mayu. Zai tsaya a filin jirgin Abuja domin nuna tambarin Nigeria Air har zuwa 28 ga Mayu, sannan ya koma Addis Ababa da safiyar 29 ga Mayu.”

Kara karanta wannan

An shiga firgici da 'yan bindiga suka kai hari a Sokoto, an kashe jami'in tsaro da sace mutane

Ya kuma ce ma’aikatan jirgin sun kasance na Ethiopian Airlines ne sanye da kayan aikinsu, yayin da gwamnatin Najeriya da 'Nigeria Air' za su yi amfani da mutanensu a yi hotuna.

A cewar Odofin, an tsara wannan nuni ne domin ya zo daidai da ranar da Sirika zai bar ofis, ta yadda za a nuna cewa ya cika alƙawarin dawo da 'Nigeria Air' da ya ɗauka.

Jirgin aro a Najeriya ya koma Ethiopia

Christopher Odofin ya kara da cewa bayan ƙasa da sa’o’i 72 da aka ajiye jirgin a Abuja, an cire tambarin Nigeria Air daga jikinsa sannan aka mayar da shi Addis Ababa.

Shaidan ya kuma ce binciken EFCC ya gano cewa 'Ethiopian Airlines' ta amince da yarjejeniyar ba da jirgin ne domin nuna tambarin Nigeria Air na kwanaki uku kacal daga 27 zuwa 29 ga Mayu, 2023.

Ya ce kwangilar kafa 'Nigeria Air' da aka ba wa kamfanin Tianaero Nigeria a watan Afrilu 2022 kan sama da Naira miliyan 299, daga baya an ƙara kuɗi zuwa sama da Naira miliyan 599 a watan Oktoba 2022 bisa umarnin Sirika.

Kara karanta wannan

Sojoji sun birkita lissafin 'yan ta'addan ISWAP, an soye ta'adda a Borno

EFCC ta gano Hadi Sirika ya yaudari ƴan Najeriya
Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukayode Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Source: Facebook

Odofin ya ce binciken wayar wani tsohon Babban Sakataren ma’aikatar ya nuna saƙon murya da Hadi Sirika ya aika daga ƙasar Spain yana umartar a tabbatar an ba wa Tianaero Nigeria kwangilar.

Kotun ta kuma karɓi takardu da dama a matsayin hujjoji, daga ciki har da wani faifan murya da ake zargin Sirika ya yi, wanda masu gabatar da ƙara suka nemi a kunna a zaman kotu na gaba.

Mai shari’a S.C. Oriji ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 17 ga Yuni, 2026 domin ci gaba da shari’ar da ake yi da tsohon ministan.

An yi zaman kotu kan Hadi Sirika

A baya, mun wallafa cewa wata babbar kotun tarayya a Abuja ta yi watsi da muhimman hujjojin hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta hukumar EFCC.

Matakin ya biyo bayan ci gaba da shari’ar zargin damfarar kwangila N2.8bn da ake yi wa Hadi Sirika da wasu mutane bayan an bayar da kwangilar sabunta 'Nigeria Air'.

Kotun ta ce bayanan da aka karɓo daga ‘yar Sirika da mijinta ba su cika sharuddan doka ba, saboda rashin bin tanadin doka da yadda ake ɗaukar bayanai a kan lamarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng