An Rage Mugun Iri: Sojojin Sun Hallaka Kwamandojin Ƴan Ta'adda, Mayaka 50
- Rundunar sojin Najeriya ta kashe manyan kwamandojin ’yan ta’adda da mayaƙa sama da 50 yayin hare-haren sama da ta kai
- Majiyoyi sun tabbatar da kwamandojin sun rasa ransu ne a hare-haren sama da aka kai yankunan Kirta da Arina Ciki na Tafkin Chadi
- Rahotanni sun nuna cewa Khalifa Umar, Abdallah da Abduljalil na cikin manyan shugabannin ’yan ta’addan da aka kashe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Maiduguri, Borno - Sojojin Najeriya ƙarƙashin Operation Hadin Kai sun samu babban nasara a yaƙin da suke yi da ta’addanci a Arewa maso Gabas.
Majiyoyin soji sun bayyana cewa an kai hare-haren ne ranar 31 ga Mayun 2026 a yankunan Kirta da Arina Ciki bayan samun sahihan bayanan sirri.

Source: Facebook
Rahoton Zagazola Makama ya ce harin ya tabbatar da kashe wasu fitattun shugabannin ’yan ta’adda da suka haɗa da Khalifa Umar, mamba a majalisar Shura daga Sigir.
Kwamandojin da aka hallaka a Borno
Haka kuma an kashe wasu kwamandojin fagen daga biyu da aka bayyana sunayensu da Abdallah da Abduljalil yayin wannan farmaki na musamman.
Majiyoyin sun ce sama da ’yan ta’adda 50 aka kashe a hare-haren, lamarin da ya ƙara raunana ƙungiyoyin da ke addabar yankin.
Baya ga kashe mayaƙan, hare-haren sun lalata wuraren ajiyar kayan aiki, cibiyoyin samar da kayayyaki da gine-ginen tallafin rayuwa na ’yan ta’addan.
Rahotanni sun nuna cewa hare-haren sama da ake kaiwa akai-akai sun sanya ’yan ta’adda cikin matsin lamba mai tsanani a yankin Tafkin Chadi.
Sakamakon hakan, da dama daga cikinsu sun bar tsibiran da suke mafaka a baya tare da komawa busassun yankuna domin kauce wa gano su.

Source: Original
Yadda ake fatattakar yan ta'adda a Borno
Wannan farmaki wani ɓangare ne na yaƙin Rundunar Operation Hadin Kai na rusa cibiyoyin ’yan ta’adda da tarwatsa hanyoyin samar musu da kayan aiki.
Har ila yau, manufar ita ce hana su ’yancin gudanar da ayyuka a sassan Arewa maso Gabashin Najeriya, cewar rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan
Sojojin Amurka sun kuma kawo farmaki Najeriya, an kashe manyan yaran Abu Mainok 3
Majiyoyin tsaro sun ce duk da cewa yankin yana cikin yanayin kwanciyar hankali, har yanzu akwai buƙatar ci gaba da sanya ido sosai.
Sun kuma nuna kwarin gwiwa kan shirin yaƙi, jajircewa da ingancin ayyukan dakarun da ke gudanar da wannan farmaki.
Ana sa ran wannan nasara za ta ƙara ƙarfafa nasarorin baya-bayan nan da sojojin Najeriya da Amurka suka samu wajen yaƙi da ta’addanci.
An kama tsohuwa mai taimakon Boko Haram
Mun ba ku labarin cewa dubun wata mata mai taimakon 'yan ta'addan ISWAP/Boko Haram ta cika bayan ta fada komar dakarun sojojin Najeriya.
Dakarun sojojin sun cafke matar ne dauke da kayayyaki wadanda ta yi niyyar kai wa ga danta wanda yake dan ta'adda ne a cikin daji.
Hukumomi sun bayyana cewa an tsare matar wadda ta kwana biyu a duniya don gudanar da bincike cikin tsanaki domin sanin mataki na gaba da za a dauka a kanta.
Asali: Legit.ng
