Akwai Matsala: Cutar Kwalara Ta Kama Mutane Sama da 4,000 a Borno, An Rasa Rayuka

Akwai Matsala: Cutar Kwalara Ta Kama Mutane Sama da 4,000 a Borno, An Rasa Rayuka

  • Rahotanni sun nuna cewa an samu karin mutane 274 da suka kamu cutar kwalara a cikin sa'o'i 24 da suka gabata a jihar Borno
  • Bayanai daga gwamnatin Borno sun nu a cewa wadanda suka kamu da cutar ta amai da gudana sun haura 4,000, kuma 39 daga cikin sun mutu
  • Gwamna Babagana Umara Zulum ya amince da raba magunguna da kayan jinya ga wuraren da ake kula da wadanda suka kamu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Borno, Nigeria - Akalla mutum 39 sun rasa rayukansu yayin da sama da mutane 4,200 ake zargin sun kamu da cutar kwalara a wasu kananan hukumomin jihar Borno.

Jami’an lafiya sun bayyana hakan ne a wani taron wayar da kai kan hanyoyin kariya da maganin zawo mai tsanani da aka gudanar a Maiduguri, babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai mummunan hari masallaci ana tsakiyar sallar Magriba a Kaduna

Borno.
Taswirar jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Cutar ta harbi karin mutane 274

Rahoton Leadership ya ruwaito shugaban cibiyar harkokin gaggawa na lafiya ta jihar, Dakta Jacob Thlizer, na cewa an samu karin mutane 274 da ake zargin sun kamu da cutar cikin sa’o’i 24 kacal.

A cewarsa, adadin wadanda ake zargi da kamuwa da kwalara ya kai mutum 4,204 a unguwanni 36 da ke cikin yankunan da annobar ta shafa.

Ya bayyana cewa adadin mutanen da suka mutu ya kai 39 zuwa lokacin da aka fitar da rahoton, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Yankunan da annobar ta fi kamari a Borno

Dakta Thlizer ya ce cutar ta bazu zuwa kananan hukumomi da dama da suka hada da Jere, Bama, Kaga, Mafa, Kwaya Kusar, Maiduguri Metropolitan Council (MMC), Konduga, Monguno, Magumeri da Ngala.

Rahoton ya nuna cewa MMC ce ke da mafi yawan masu dauke da cutar da mutum 2,404, sai Jere da mutum 1,214.

Kara karanta wannan

Za a yi auren gata a Kano, 'yan mata, zawarawa da samari 3,000 za su angwance

Gwamnati ta dauki matakan gaggawa

Jami’an lafiya sun bayyana cewa gwamnatin Borno ta fara daukar matakan dakile yaduwar cutar.

Daga cikin matakan akwai kafa tsarin gudanar da ayyukan gaggawa, gudanar da taruka da abokan hulda a bangaren lafiya, wayar da kan jama'a da kuma samar da magunguna da kayan aikin jinya.

Gwamna Babagana Zulum.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum Hoto: @ProfZulum
Source: Facebook

Gwamna Zulum ya ware magunguna

Sakataren ma’aikatar lafiya ta jihar, Shetima Muhammad, ya ce an ware cibiyar kula da cututtuka masu yaduwa da ke Njimtilo da kuma sansanin kula da marasa lafiya a Ngarannam mai gado sama da 1,000 domin kula da masu fama da cutar.

Ya kara da cewa Gwamna Babagana Umara Zulum ya amince da raba magunguna da kayan jinya ga wuraren da ake kula da wadanda suka kamu.

Jami’an gwamnati sun bukaci mazauna jihar su rika kula da tsaftar muhalli da ta abinci, su rika amfani da ruwa mai tsafta, sannan su garzaya asibiti idan sun fara ganin alamomin kwalara.

NCDC ta yi gargadi kan cutar Ebola

Kara karanta wannan

DSS ta kama yan kasar waje da wasu da ake zargi da sace dalibai 300 a Neja

An ji cewa hukumar yaki da yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta sanya Legas, Kano, Rivers da wasu jihohi cikin shirin ko-ta-kwana kan cutar Ebola.

A cikin sanarwar lafiya ta kasa da ta aika wa kwamishinonin lafiya a fadin kasar, hukumar ta gargadi cewa Najeriya na cikin hadarin shigowar cutar.

NCDC ta ce cutar za ta iya bulla a jihohin ne saboda filayen jiragen sama na kasa da kasa da suke da shi, tashoshin ruwa, iyaka da kasashe da yawan zirga-zirgar jama’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262