Tashin Hankali: An Harbe Jami'in Tsaron Najeriya har Lahira, An Sace Ƴarsa a Kogi

Tashin Hankali: An Harbe Jami'in Tsaron Najeriya har Lahira, An Sace Ƴarsa a Kogi

  • Wasu miyagun ‘yan bindiga sun kashe jami’in NSCDC, Ayo Olukotun, tare da sace diyarsa da wasu mutane a jihar Kogi
  • Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kai farmaki garin Odo-Ere, inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi tare da kashe jami'in
  • Ciyaman da kuma dan majalisar tarayya mai wakiltar yankin sun yi Allah wadai da harin tare da aika sakon gaggawa ga jami'an tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kogi - Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kashe wani jami’in rundunar tsaro ta NSCDC mai suna Ayo Olukotun tare da yin garkuwa da diyarsa da wasu mutane.

Rahoton ya nuna cewa an kashe jami'in NSCDC din tare da sace 'yarsa ne a garin Odo-Ere da ke karamar hukumar Yagba West a jihar Kogi.

Kara karanta wannan

Rikicin NDC: Abin da Kwankwaso da Seriake Dickson suka tattauna a zaman Abuja

'Yan bindiga sun kashe jami'in hukumar NSCDC
Jami'an hukumar tsaron farar hula (NSCDC). Hoto: @official_NSCDC
Source: Twitter

'Yan bindiga sun kashe jami'in tsaro

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa 'yan bindigan sun kai harin ne da misalin karfe 8:30 na dare a ranar Litinin, inda suka rika harbi kan mai uwa da wabi.

An ce mutane da dama sun ranta a na-kare domin neman mafaka yayin da maharan suka shiga cikin garin.

Majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa maharan sun kutsa gidan jami’in NSCDC din, inda suka harbe shi tare da yin awon gaba da diyarsa da wasu mutane zuwa cikin daji.

Wata majiya daga garin ta ce an garzaya da Olukotun zuwa asibiti bayan harin, inda a nan ne likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.

Majiyar ta ce:

“An kai Mista Olukotun asibiti cikin gaggawa bayan harin, likitocin da suke a bakin aiki ne suka tabbatar da ya rasu. Yanzu haka an kai gawarsa dakin ajiye gawa."

Ciyaman ya yi alhinin kisan jami'in

Kara karanta wannan

An shiga firgici da 'yan bindiga suka kai hari a Sokoto, an kashe jami'in tsaro da sace mutane

Shugaban karamar hukumar Yagba ta Yamma, Hon. Tosin Olokun, ya yi Allah wadai da harin, yana mai bayyana lamarin a matsayin abin takaici da ban tausayi.

Olokun, wanda shi ne shugaban kungiyar ALGON reshen jihar Kogi, ya ce rasuwar jami’in ta kasance babban rashi ga iyalansa da al’ummar Odo-Ere da ma daukacin karamar hukumar.

A wata sanarwa da sakataren yada labaransa, Adeyemi Babarinde ya fitar, shugaban karamar hukumar ya ce:

“Mun shiga cikin jimami saboda wannan mummunan lamari. A madadin gwamnati da al’ummar Yagba ta Yamma, ina mika ta’aziyya ta ga iyalan Mista Ayo Olukotun da daukacin wadanda abin ya shafa."
An ce 'yan bindiga sun harbe jami'in tsaron NSCDC har lahira a Kogi
Taswirar jihar Kogi, inda 'yan bindiga suka kashe jami'in NSCDC, suka sace 'yarsa. Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Dan majalisar Kogi ya yi martani

Shi ma dan majalisar wakilai mai wakiltar Yagba ta Gabas, Yagba ta Yamma da Mopamuro, Hon. Leke Joseph Abejide, ya bayyana harin a matsayin abin takaici.

Abejide ya ce mutuwar jami’in da sace diyarsa sun jefa al’ummar yankin cikin bakin ciki, in ji rahoton Daily Post Nigeria.

“Labarin kashe Mista Ayo da sace diyarsa ya girgiza ni matuka. Wannan lokaci ne mai matukar wahala ga al’ummar Odo-Ere da jihar Kogi baki daya,” in ji Hon. Leke Joseph.

Kara karanta wannan

Asirin matar aure ya tonu, an gano tana sheke aya a otal bayan an tara N20m kudin fansa

'Dan majalisar ya bukaci Gwamnatin jihar Kogi da jami’an tsaro su kara kaimi wajen ceto wadanda aka sace musamman diyar jami’in da aka kashe.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan harin ba.

'Yan bindiga sun kashe jami'an NSCDC

A wani labari, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe jami’an hukumar NSCDC guda takwas a Edo.

'Yan bindigan sun kuma yi garkuwa da wani ɗan kasar China a harin da suka kai a garin Okpella, karamar hukumar Etsako ta Gabas ta jihar Edo.

Majiyoyi sun ce maharan, waɗanda ke ɗauke da manyan makamai, sun buɗe wuta kai tsaye kan jami’an tsaron, inda suka kashe guda takwas a wurin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com