Sojoji Sun Birkita Lissafin 'Yan Ta'addan ISWAP, an Soye 'Yan Ta'adda a Borno
- 'Yan ta'addan kungiyar ISWAP sun gane shayi ruwa ne bayan da dakarun sojoji Najeriya suka kai masu hare-hare a Borno
- Dakarun sojojin sun farmaki 'yan ta'addan wadanda ke cikin motoci yayin da suke zirga-zirga a Arewacin jihar Borno
- Hare-haren sun yi sanadiyyar hallaka 'yan ta'addan ISWAP tare da lalata motocin da suke amfani da su a cikin daji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Borno - Bangaren dakarun sama na rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) ya kashe aƙalla mutane tara da ake zargi 'yan ta'addan ƙungiyar ISWAP (Islamic State West Africa Province) ne a jihar Borno.
Dakarun sojojin sun lalata motoci da dama a lokacin wasu hare-haren sama da aka kai a kewayen Cross Kauwa da Ali Sherifti da ke Arewacin jihar Borno.

Source: Twitter
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
Sojoji sun ragargaji 'yan ISWAP
Farmakin wanda ya fara ranar Asabar, 6 ga watan Yuni, ya karkata ne ga 'yan ta'addan da ke ƙoƙarin sake samun matsuguni a cikin yankin tafkin Chadi.
Majiyoyi sun shaida wa kafar cewa an fara aikin ne bayan wani tsarin tattara bayanan sirri, sa ido, da bincike ya hango zirga-zirga a wani sansanin sirri da ake zargin na 'yan ta'adda ne a Cross Kauwa.
Binciken ya ya gano kusan motoci 12 da aka ɓoye a ƙarƙashin bishiyoyi, yayin da aka hango mutanen da ake zargi 'yan ta'addan ne suna zirga-zirga a tsakanin mafaka domin guje wa hango su.
An gano maboyar 'yan ta'adda
Ganowar ta nuna abin da ke bayyana a matsayin babban wurin taron 'yan ta'adda da ake amfani da shi don samar da kayayyakin aiki, daidaita zirga-zirga, da yiwuwar tsara hare-hare.
Bayan tabbatar da ayyukan 'yan ta'addan da kuma samun amincewa daga kwamandojin yaki, wani jirgin yaƙi ya kai kwararren hari kan wasu gungun motoci a cikin mafakar.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Borno ta yi maganar biyan Boko Haram kudin fansa kafin a ceto mutane 360
Makamin ya daki wurin daidai cikin kwarewa, wanda hakan ya yi sanadiyyar sauka kai tsaye a kan motoci guda huɗu.
Karin sa ido ya gano zirga-zirga a kewayen wurin, ciki har da motoci uku da ke ƙoƙarin janyewa da kuma mayaƙa da dama da ke neman mafaka.

Source: Original
Dakarun Sojoji sun kashe 'yan ISWAP
Aikin ya canza alƙibla zuwa yankin Ali Sherifti bayan samun bayanan sirri na cewa mayakan ISWAP suna shirya hare-hare a kan al'ummomin da ke makwabtaka da su.
Daga bisani jirgin ya gano mutane takwas da ake zargi 'yan ta'adda ne da suka ɓoye a ƙarƙashin wata bishiya, inda ya kai harin kwarewa wanda ya kashe mutum biyar daga cikinsu.
An kuma kashe wasu 'yan ta'adda guda huɗu daban da ke tafiya zuwa wata mota da aka ɓoye, sannan aka lalata motar baki ɗaya.
Sojoji sun cafke jagoran 'yan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun rundunar sojojin Najeriya sun kama wani da ake zargi da kasancewa jagoran ‘yan ta’adda mai suna Kachalla Halilu.

Kara karanta wannan
Yadda sojoji suka yi wa 'yan Boko Haram dabara wajen ceto mutane 360 da aka sace a Borno
Bayanai sun nuna cewa an kama Kachalla Halilu ne bayan farmaki da aka kai a kasuwar Shinkafi da ke jihar Zamfara sakamakon samun bayanan sirri.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa dakarun sojojin sun tura jami’ansu zuwa kasuwar Shinkafi bayan hango Kachalla Halilu.
Asali: Legit.ng
