Kofin Duniya: Trump Ya Yi wa Tawagar 'Yan Kwallon Iran Rashin Mutunci a Amurka

Kofin Duniya: Trump Ya Yi wa Tawagar 'Yan Kwallon Iran Rashin Mutunci a Amurka

  • Hukumar ƙwallon ƙafa ta Iran ta ce Amurka ta soke rabon tikitin da aka ware mata domin wasannin rukunin farko na gasar kofin duniya a Amurka
  • Ta zargi Amurka mai masaukin baki da hana magoya bayan Iran halartar wasannin a yayin da ake ci gaba da takun-saƙa mai tsanani tsakaninsu
  • Amurka ta gindaya wasu sharuda ga Iran a babbar gasar ƙwallon ƙafa ta duniya, ciki har da ƙin ba wasu daga cikin ma’aikatan kasar biza

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran - ’Yan wasan Iran da suka samu bizar Amurka sun isa Mexico ranar Lahadi domin buga gasar kofin duniya, amma yanzu makomar magoya bayan ƙungiyar na cikin rashin tabbas.

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Iran ta ce Amurka ta soke yawan adadin tikitin da aka ware wa ƙungiyar ƙasar domin wasannin rukunin farko na kofin duniya.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya fusata kan rashin tsaro, ya ragargaji Tinubu

"Yan wasan Iran da magoya bayan su
'Yan kwallon Iran bayan fafatawa da Uzbekistan a 2025. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Kofin duniya: Iran ta zargi Amurka

Al Jazeera ta wallafa cewa Iran ta zargi Amurka da hana magoya bayan Tehran halartar wasannin da za ta yi a gasar kofin duniya saboda tsamin dangantakar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.

“Saura ƙasa da kwana uku kafin fara gasar Kofin Duniya ta 2026 ... Amurka ta sake ɗaukar matakin hana magoya bayan Iran halartar filayen wasannin da ƙungiyar za ta buga wasanninta uku na matakin rukunin farko,”

In ji FFIRI a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Talata.

Amurka ta sanya wasu sharuda ga Iran a wannan babbar gasar ƙwallon ƙafa ta duniya, ciki har da ƙin ba wasu daga cikin ma’aikatan Iran biza, yayin da ƙasashen biyu ke ci gaba da kasancewa cikin yanayin yaƙi.

'Yan wasan kasar Iran
'Yan kwallon kafar Iran suna daukar horo a filin wasa. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Dokar da FIFA ta saka kan tikiti

Hukumar ƙwallon ƙafar Iran ta ce dokokin FIFA sun tanadi cewa a ware mata kashi 8 cikin 100 na tikitin kowane wasa, waɗanda ake bai wa ƙungiyoyin ƙasashe masu shiga gasar domin rarrabawa magoya bayansu ta hanyoyin hukuma.

Kara karanta wannan

Ndume: Sanata ya faɗi wurin da ya dace Amurka ta kafa sansanin soji a jihar Borno

A cewar sanarwar, FFIRI ta riga ta fara sayar da tikitin wasannin rukunin farko da New Zealand, Belgium da Masar bayan ta karɓi nata kaso, kuma wasu daga cikin magoya baya sun riga sun kammala shirye-shiryensu.

Times of Israel ta wallafa cewa sanarwar ta ce:

“Sai dai a wani mataki da ba a zata ba, an janye adadin da aka bai wa hukumar kwallon kafar Iran, kuma a halin yanzu hukumar ba za ta iya samar da ko tikiti guda ɗaya ga magoya bayan ƙungiyar ba,”

In ji sanarwar.

Trump na son dakatar da yakin Iran

A wani labarin, kun ji cewa shugaban Amurka Donald Trump ya kira Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu a ranar Litinin kan yaki da Iran.

Hakan ya biyo bayan musayar hare-hare tsakanin Isra’ila da Iran tun bayan yarjejeniyar tsagaita wuta da aka kulla a watan Afrilun 2026.

Biyo bayan kiran, Trump ya bukaci Iran da Isra'ila su tsagaita wuta, yana mai cewa za a koma teburin sulhu domin tabbatar da zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng