Rikicin NDC: Abin da Kwankwaso da Seriake Dickson Suka Tattauna a Zaman Abuja

Rikicin NDC: Abin da Kwankwaso da Seriake Dickson Suka Tattauna a Zaman Abuja

  • Jagororin ƙungiyar Kwankwasiyya sun gana da shugabannin NDC domin warware saɓanin cikin gida da ya bullo a jihar Kano
  • Jagoran NDC, Henry Seriake Dickson, ya gana da masu takun-saƙa a bayan rahoton Rabi'u Musa Kwankwaso zai iya barin jam'iyya
  • NDC ta ce ba za ta kakaba 'yan takara ba, kuma har yanzu ba ta fitar da sakamakon zaɓen fitar da gwani a kowace jiha ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Wata tawaga a ƙarƙashin jagorancin shugaban Kwankwasiyya na ƙasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ta ziyarci jagoran NDC Henry Seriake Dickson.

Bangarorin biyu sun shiga wani taron sirri domin nemo mafita ga rikice-rikicen cikin gida da suka dabaibaye jam’iyyar a jihar Kano.

Kara karanta wannan

NNPP ta zargi Kwankwaso da yi mata kamun kazar kuku, ta mika bukata ga INEC

Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da jagororin NDC sun zauna a Abuja
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, Seriake Dickson da Kwamred Aminu Abdussalam Gwarzo bayan ganawa a Abuja Hoto: Hon Saifullahi Hassan
Source: Facebook

TVC News ta wallafa cewa taron, wanda ya haɗa da shugabannin NDC na ƙasa, ya gudana ne da daddare a Talata, 9 ga watan Yuni, 2026 inda aka tattauna matsalolin da suka taso tsakanin ɓangaren Kwankwasiyya da wasu tsofaffin jiga-jigan jam’iyyar a jihar.

NDC, Kwankwasiyya sun zauna a Abuja

Rahoton Daily Post ga ce a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na ƙasa na NDC, Osa Director, ya fitar, an bayyana cewa taron ya mayar da hankali ne kan samar da haɗin kai.

Haka kuma an ƙara mayar da hankali a kan batun ba wa kowa damar shiga harkokin jam’iyya da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƴan NDC kafin fara wasu muhimman tsare-tsaren cikin gida.

Sanarwar ta ce shugabannin NDC na ci gaba da shiga tsakani domin sauraron koke-koken da ke akwai tare da tabbatar da cewa an mutunta ƙa’idodin dimokuraɗiyya.

Jam'iyyar NDC ta yi alkawarin yin adalci

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya fusata kan rashin tsaro, ya ragargaji Tinubu

Jam’iyyar NDC ta jaddada cewa ba za ta kakaba wa ƴaƴanta 'yan takara a jihar Kano ba ko kuma a sauran sassan ƙasar nan.

Sanarwar ta ce jam’iyyar na daraja ƙa’idojin dimokuraɗiyyar cikin gida, kuma za ta tabbatar da gudanar da sahihin tsari mai gaskiya da adalci wajen zaɓen cikin gida

NDC ta Ce ba za ta ƙaƙabawa ƴaƴanta ƴan takara ba
Seriake Dickson, jagoran NDC na kasa a yayin wani jawabi a taron jam'iyya Hoto: Henry Seriake Dickson
Source: Facebook

Ta ce:

“Shugabancin NDC ba zai kakaba wa ƴaƴanta 'yan takara ba a jihar Kano ko kuma a faɗin ƙasa baki ɗaya, domin jam’iyyar na mutunta ƙimar dimokuraɗiyyar cikin gida.”

Har ila yau, jam’iyyar ta musanta rahotannin da ke cewa an riga an fitar da sakamakon zaɓen fitar da gwani a wasu jihohi.

NDC ta yi kira ga jama’a da su yi watsi da duk wata jerin sunaye ko sakamakon zaɓe da ake yaɗawa, tana mai cewa ba ta amince da irin waɗannan bayanai ba.

Jam’iyyar ta ƙara da cewa zaman da aka yi na sa’o’i da dama ya yi amfani, kuma yana daga cikin matakan da ake ɗauka domin ƙarfafa tsari da daidaita harkokin cikin gida a jam’iyyar kafin manyan matakai masu zuwa.

Kara karanta wannan

Gawuna na shirin komawa ADC daga NDC, ya mika bukatunsa ga jam'iyyar

A bangaren Kwankwasiyya, an ga Aminu Abdussalam Gwarzo da Nasiru Sule Garo, sai dai ba a ga duriyar Nasiru Gawuna da ake jita-jitar zai iya koma wa NDC ba.

Kwankwaso ya faɗi alakarsa da Obi

A baya, mun wallafa labarin cewa ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a NDC, Sanata Rabiu Kwankwaso ya ce shi da Peter Obi na da abubuwa da dama iri ɗaya.

Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da rade-radin cewa an fara samun baraka a jam'iyyar NDC da Kwankwaso ke ciki, ana cewa zai iya komawa wata tafiyar siyasa.

Sanata Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa babban burin su shi ne a samu a ci zabe domin kawo cigaba mai dorewa a Najeriya a bangarori da suka shafi 'yan kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng