"Sau 3 kacal na ga Ƴaƴana," Zulum Ya Tuno abin da Ya Faru da Shi bayan Zaben 2019

"Sau 3 kacal na ga Ƴaƴana," Zulum Ya Tuno abin da Ya Faru da Shi bayan Zaben 2019

  • Babagana Umara Zulum ya bayyana cewa sau uku kacal ya ga 'ya'yansa a cikin kwanaki 55 bayan rantsar da shi a matsayin Gwamnan Borno
  • Mai girma Zulum ya ce kalubalen tsaro shi ne mafi wahalar da gwamnatinsa ta fuskanta tun bayan hawansa mulki a shekarar 2019
  • Gwamnan ya nuna cikakken goyon baya ga dan takarar APC, Mustapha Gubio, yana mai bayyana shi a matsayin mutum mai gaskiya da nutsuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana irin sadaukarwar da ya yi bayan hawansa mulki a shekarar 2019 domin tunkarar matsalolin tsaro da na jin kai da suka addabi jihar.

Zulum ya ce cikin kwanaki 55 na farko bayan rantsar da shi a matsayin gwamna, ya samu damar ganin ‘ya’yansa sau uku ne kawai saboda yawan ayyuka da matsin lambar shugabanci.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: An hallaka mawaki dan asalin Najeriya a Burtaniya

Gwamna Babagana Zulum ya tuno da abin da ya faru a shekarar da ya karbi mulki.
Gwamnan Borno Babagana Zulum yana jawabi a lokacin da ya karbi bakuncin Mustapha Gubio a Maiduguri. Hoto: @dauda_iliya
Source: Twitter

Zulum ya tuno da hawansa mulki a 2019

Ya bayyana hakan ne yayin da yake karbar bakuncin manyan ‘ya’yan karamar hukumar Gubio da suka kai masa ziyarar girmamawa tare da dan takarar gwamnan APC, Mustapha Gubio, in ji rahoton Daily Trust.

Gwamnan ya ce shekarun farko na mulkinsa sun kasance masu matukar wahala sakamakon matsalar Boko Haram da rikicin jin kai da suka addabi jihar Borno.

A cewarsa, shugabanci a irin wannan yanayi na bukatar sadaukarwa da hakuri domin tabbatar da zaman lafiya da cigaban jama’a.

Zulum ya ce:

“Lokacin da na karbi ragamar mulkin jihar, cikin kwanaki 55 na farko na mulkina, na ga ‘ya’yana sau uku ne kacal. Shekaru hudu na farko sun kasance masu matukar wahala, amma Allah Madaukakin Sarki ya taimaka mana muka fara ganin haske.”

Ya kara da cewa matsalar tsaro ita ce mafi girman kalubalen da gwamnatinsa ke fuskanta.

Alkawarin Zulum kan zaman lafiya a Borno

Kara karanta wannan

Shugaba a majalisa ya faɗi lokacin da za a amince da dokar ƴan sandan jihohi

Babagana Zulum ya bayyana cewa gwamnatinsa na ci gaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya da cigaban jihar kafin ya sauka daga mulki.

Ya nuna kwarin gwiwa cewa kafin karewar wa’adinsa, jihar Borno za ta kasance cikin yanayi mafi kyau ta fuskar tsaro da tattalin arziki.

“Insha Allah kafin na bar mulki, halin da ake ciki zai fi na yanzu kyau. Zan mika gwamnati mai karfi, wadata da zaman lafiya ga Injiniya Mustapha Gubio,” in ji Zulum.
Gwamna Zulum ya yabawa Gubio yayin da ake tunkarar zaben 2027.
Tawagar Mustapha Gubio, dan takarar gwamnan Borno na APC lokacin da suka ziyarci Gwamna Babagana Zulum a gidan gwamnati. Hoto: @dauda_iliya
Source: Twitter

Zulum ya yabawa Mustapha Gubio

Jaridar The Nation ta rahoto Zulum ya bayyana Mustapha Gubio a matsayin mutum mai gaskiya, tawali’u da nutsuwa wanda ya dade yana sani tun lokacin da yake dalibi a jami’ar Maiduguri.

A cewarsa, ya san Gubio sama da shekaru 26 kuma yana da yakinin cewa zai iya jagorantar jihar cikin nasara idan aka zabe shi.

“Na san Alhaji Mustapha Gubio tsawon shekaru 26 tun yana dalibi a jami’ar Maiduguri. Mutum ne mai gaskiya, tausayi da natsuwa. Allah zai taimaka masa wajen jagorantar jihar Borno."

- Gwamna Babagana Zulum.

Kara karanta wannan

Amurka ta gamu da matsala, jirgin yakinta ya rikito a kusa da mashigar Hormuz

Zulum ya goyi bayan takarar Gubio

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Gwamna Babagana Umara Zulum ya yi abin mamaki yayin da ya bayyana wanda yake so ya gaje shi a zaben 2027.

Mustapha Gubio, tsohon kwamishinan ayyuka ne Gwamna Zulum ya nuna wa cikaken goyon bayansa donya dare kujerar gwamna da nufin dora wa a inda ya tsaya.

Wannan mataki ya fara tada kura a cikin jam'iyyar APC ta jihar, inda masu sharhi ke hango takun-saka tsakanin sansanin Zulum da na Kashim Shettima.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com