Bayan Yaudara na Shekaru, Tinubu Ya Ƙaddamar da Gyaran Hanyar Gombe zuwa Maiduguri

Bayan Yaudara na Shekaru, Tinubu Ya Ƙaddamar da Gyaran Hanyar Gombe zuwa Maiduguri

  • Bayan shafe shekaru ana banza da lamarin, Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da aikin sake gina babbar hanyar Gombe zuwa Biu da Maiduguri
  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa an shafe shekaru masu yawa na alkawura da kwangilolin amma ba a kai ga kammala su ba
  • Ministan ayyuka, David Umahi, ya ce aikin yana cikin shirye-shiryen manyan ayyukan gwamnatin Bola Tinubu domin bunkasa sufuri, kasuwanci da ci gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da aikin sake gina babbar hanyar Gombe zuwa Biu da Maiduguri saboda muhimmancinta.

Mutane da dama daga yankin kama daga mazauna, direbobi da 'yan kasuwa a Arewa maso Gabas suka ce sun gaji da alkawuran da ake yi.

An ƙaddamar da sake gyara hanyar Gombe zuwa Maiduguri
Ministan ayyuka, Dave Umahi yayin ziyarar ƙaddamar da hanyar Gombe zuwa Maiduguri tare da Gwamna Inuwa Yahaya. Hoto: Isma'ila Uba Misilli.
Source: Facebook

A ranar Alhamis 4 ga watan Yunin 2026, sakataren yada labaran Gwamnan Gombe, Isma'ila Uba Misilli ya wallafa a Facebook cewa gwamnatin tarayya ta kaddamar da aikin a Gombe.

Kara karanta wannan

Umahi: Tinubu ya tattare manyan ayyukan tituna a Arewa

Bayan shekaru, an ƙaddamar da hanyar Gombe-Maiduguri

Gwamnatin tarayya ta bayyana shirin aikin a matsayin muhimmin bangare na shirin sabunta ababen more rayuwa.

A tsawon shekaru da dama, gwamnatoci daban-daban sun bayar da kwangilolin gyaran hanyar, amma yawancin ayyukan sun tsaya cik ko kuma ba su kammala ba.

Sakamakon haka, masu amfani da hanyar sun ci gaba da fuskantar wahalhalu, hadurran hanya da kuma tsadar sufuri sakamakon mummunar lalacewar titin.

Hanyar ta hada Gombe da kudancin Borno tare da Maiduguri, kuma ta kasance cikin mawuyacin hali duk da kwangiloli da aka bayar a baya.

Buhari ya ba da kwangilar hanyar a 2017

Rahotanni sun nuna cewa daya daga cikin manyan kokarin gyaran hanyar ya faru ne a shekarar 2017 lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A lokacin, an ce an bayar da kwangilar aikin kan kudi kimanin Naira biliyan 27.23, amma daga baya aka yi watsi da ita, cewar Premium Times.

Ministan Ayyuka, David Umahi, ya ce gwamnatin Bola Tinubu ta kuduri aniyar kammala aikin yadda ya kamata domin amfanin al'umma.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace tsohon shugaban APC, sun masa bidiyo yana neman agaji

Ya bayyana cewa titin mai tsawon kilomita 125 mai hanya biyu wani bangare ne na babban layin kilomita 420 daga Akwanga zuwa Borno.

Umahi ya kara da cewa Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da aikin a matsayin kashi na hudu na manyan ayyukan gwamnatin Tinubu.

A cewarsa, aikin ba wai gina hanya kawai ba ne, har ila yau yana hada al'ummomi da samar da sababbin damar tattalin arziki.

Gwamna Inuwa ya yabawa gwamnatin Tinubu
Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe yana jawabi. Hoto: Ismaila Uba Misilli.
Source: Facebook

Martanin Gwamna Inuwa Yahaya na Gombe

Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana fara aikin a matsayin babban ci gaba ga yankin Arewa maso Gabas.

Ya ce lalacewar hanyar ta jima tana damun mazauna yankin, masu safara da 'yan kasuwa saboda matsalolin zirga-zirga.

Abin da mazauna yankin ke tunani

Duk da haka, wasu mazauna yankin sun karbi sanarwar da taka-tsantsan saboda gazawar alkawuran da suka gabata.

Masu safara, 'yan kasuwa da matafiya na fatan wannan karon aikin zai kawo karshen matsalolin da suka dade suna fuskanta.

Sai dai mazauna yankin sun ce za su auna nasarar aikin ne ta hanyar ganin ci gaban aiki a fili, ba ta kaddamarwa kadai ba.

Kara karanta wannan

An samu hirar Trump da jami'ansa da ke nuna fargabar yaki da Iran

Yadda Gwamnatin Tinubu ta hana Najeriya durkushewa

An ji cewa shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatin sa ta ɗauki matakai masu wahala domin ceto tattalin arzikin Najeriya daga durƙushewa.

Ya bayyana cewa an samu ci gaba a fannoni kamar hanyoyi, ilimi, noma, gidaje da makamashi cikin shekaru uku da ya yi a karagar mulkin kasar.

Tinubu ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa sadaukarwar da suka yi ba ta tafi a banza ba domin ƙasar na dawowa cikin hayyacinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.