Sanata Ndume Ya Jinjina wa Tinubu, Ya Ce 'Yan Arewa Za Su Saka Masa da Kuri'u a 2027

Sanata Ndume Ya Jinjina wa Tinubu, Ya Ce 'Yan Arewa Za Su Saka Masa da Kuri'u a 2027

  • Sanata Ali Ndume ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa amincewa da aikin titin Gombe zuwa Biu tare da fadada shi
  • Ndume ya bayyana cewa aikin zai taimaka wajen bunkasa harkokin tattalin arziki da zirga-zirga a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya
  • 'Dan Majalisar dattawan ya ce mutanen yankin za su saka wa Tinubu da kuri'unsu a zaben shekarar 2027 mai zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Borno, Nigeria - Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya yabawa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa amincewa da sake ginawa tare da fadada titin Gombe zuwa Biu.

A ranar Alhamis ne gwamnatin tarayya ta kaddamar da aikin sabuntawa da kuma mayar da titin Gombe-Biu mai tsawon kilomita 125 zuwa hanya mai layi biyu, kan kudi tiriliyan 1.245.

Snaata Ndume.
Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu a Majalisar dattawa, Muhammad Ali Ndume Hoto: Muhammad Ali Ndume
Source: Facebook

Aikin titin zai bunkasa tattalin arziki

Kara karanta wannan

Tsohon ɗan takara a ADC ya fice daga jam'iyyar, ya koma layin Pantami a PDP

The Cable ta ce a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, Ndume ya bayyana cewa aikin zai taimaka wajen bunkasa harkokin kasuwanci, saukaka zirga-zirga da kuma inganta tsaro a yankin Arewa maso Gabas.

Sanatan ya ce ya shafe shekaru yana kira ga gwamnatoci daban-daban da su gyara hanyar saboda muhimmancinta ga al'ummar yankin.

Yadda Ali Ndume ya nemi a gyara titin

Ndume ya tuna cewa tun a shekarar 2019 ya gabatar da koken halin da hanyar ke ciki yayin wata ganawa da tsohon Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Raji Fashola.

A cewarsa:

"Na bayyana mummunan halin da titin Biu-Gombe ke ciki tare da jaddada muhimmancinta a harkokin tattalin arzikin yankin, saukaka zirga-zirga tsakanin jihohi, ayyukan tsaro da ci gaban yankin Arewa maso Gabas."

Ya kara da cewa a watan Yulin 2021 ya sake gabatar da bukatar sanya hanyar cikin manyan ayyukan da gwamnatin tarayya za ta ba fifiko wajen gyarawa.

Wasikar da sanatan ya rubuta wa Umahi

Ndume ya ce wasikar da ya aika wa Ministan Ayyuka, David Umahi, a ranar 11 ga Fabrairu, 2026 ta taimaka wajen ganin an amince da aikin.

Kara karanta wannan

Bayan yaudara na shekaru, Tinubu ya ƙaddamar da gyaran hanyar Gombe zuwa Maiduguri

Ya bayyana cewa a cikin wasikar ya nuna damuwarsa kan yadda aka cire titin Biu/Damboa/Maiduguri daga cikin manyan ayyukan gwamnatin tarayya na shekarar 2026.

A cewarsa, daga bisani Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da aikin karkashin tsarin tallafin haraji da ayyukan more rayuwa.

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana aiki a ofishinsa da ke fadar gwamnatin Najeriya Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Ya bukaci a tsawaita titin zuwa Maiduguri

Sanata Ndume ya yi kira ga shugaban kasa da ya kara fadada aikin daga Biu zuwa Maiduguri, Monguno, Ngala da kuma Yola, cewar rahoton Guardian.

Ya bayyana cewa al'ummar Arewa maso Gabas za su yaba da wannan aikin da gwamnatin Tinubu ta fara ta hanyar saka masa da kuri'unsu a zaben 2027.

Ndume ya hango hanyar dawo da tsaro

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Ali Muhammad Ndume ya bayyana yadda gwamnatin Najeriya za ta kawo karshen ta'addanci idan ta shirya da gaske.

Ndume ya bayyana cewa Najeriya na da damar kawo ƙarshen matsalar tsaro cikin watanni shida kacal idan gwamnatin tarayya ta nuna ƙwazo.

Ya kuma dora alhakin matsalar tsaro kan rashin bin tsare-tsaren da aka amince da su a baya, yana mai cewa dole ne gwamnati ta tabbatar da aiwatar da manufofi yadda ya kamata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262