Atiku Ya Yi Murna da Ceto Mutane 360, Ya Ce Sojoji Za Su Iya Murkushe Ta'addanci a Najeriya
- 'Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar ya yi murna da ceto mutum 360 da aka sace a Ngoshe da ke jihar Borno
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yabawa sojoji da jami’an tsaro kan nasarar da suka samu na ceto mutanen bayan watanni fiye da biyu
- Ya ce hakan ya nuna cewa dakarun tsaron Najeriya za su iya magance duk wata barazana matukar aka samar masu da kayan aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Borno, Nigeria - Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma 'dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar, ya nuna farin cikinsa kan ceto mutane 360 da aka yi garkuwa da su a Ngoshe, jihar Borno.
Atiku ya ce wannan nasara ta kawo karshen wahalar da wadanda aka sace da iyalansu suka shafe watanni suna ciki tun bayan garkuwa da su a watan Maris da ya gabata.

Source: Twitter
Hakan na kunshe ne a cikin wani sako da Atiku ya wallafa a shafinsa na X a jiya Litinin, 8 ga watan Mayu, 2026.
Atiku Abubakar ya yaba wa jami’an tsaro
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yaba wa rundunar sojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro da suka taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da aikin ceton.
Ya ce wannan nasara ta nuna cewa jami’an tsaron kasar na da kwarewa da karfin da za su iya kawo karshen matsalar tsaro idan aka samar musu da kayan aiki da kuma ingantaccen shugabanci.
A cewarsa, rikicin ta’addanci da ya addabi Najeriya tsawon kusan shekaru 20 zai iya zama tarihi idan aka kara bai wa jami’an tsaro cikakken goyon baya.
Ya bukaci a ceto daliban Oyo, Borno
Duk da yabon da ya yi kan ceto mutanen Ngoshe, Atiku ya nuna cewa har yanzu akwai babban aiki a gaba saboda wasu ’yan Najeriya na ci gaba da kasancewa a hannun masu garkuwa da mutane da ’yan ta’adda.

Kara karanta wannan
Matsalar tsaro: NLC da TUC sun yi barazanar hana ma'aikata zuwa wurin aiki a Najeriya
Ya bukaci gwamnati da jami’an tsaro su kara kaimi wajen kubutar da kusan dalibai da malamai 100 da aka sace a yankin Oriire na jihar Oyo da kuma Mussa a jihar Borno.
Atiku ya ce ya kamata a yi amfani da wannan nasara a matsayin karin kwarin gwiwa wajen ceto sauran mutanen da ke tsare a hannun masu garkuwa.

Source: Twitter
Kiran sake fasalin tsarin tsaro
Hakazalika, Atiku ya yi kira da a sake fasalin tsarin tsaron Najeriya ta yadda za a fi mayar da hankali kan tattara bayanan sirri, amfani da fasahar zamani da kuma daukar matakan kariya kafin hare-hare su faru.
Ya ce matakan kariya da gano barazana tun kafin ta afku su ne mafi dacewa wajen dakile ayyukan ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a fadin kasar.
Atiku ya soki tsarin tsaron Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya soki yadda gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke tafiyar da sha'anin tsaro.
Ya buƙaci Gwamnatin tarayya da ta hanzarta gudanar da cikakkiyar bita kan tsarin manufofin yaƙi da ta'addanci na Najeriya.
Atiku ya ce ya kamata Gwamnatin tarayya ta rika nazari tare da daukar darussa daga hare-haren 'yan ta'adda domin sauya salo da dabarun yaki da ta'addanci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
