Jerin Gwamnonin Arewa da Suka Fitar da Wadanda za Su Gaje Su a Zaben 2027

Jerin Gwamnonin Arewa da Suka Fitar da Wadanda za Su Gaje Su a Zaben 2027

Yayin da zaben shekarar 2027 ke kara karatowa, gwamnonin da za su sauka daga mulki sun fara ayyana wadanda suke fatan su gaje su.

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Batun zaben 2027 na cigaba da daukar hankali musamman bayan gwamnonin jihohi sun fara ayyana wadanda suke so su gaje su.

Hakan na zuwa ne yayin da jam'iyyun APC, PDP da sauransu suka fara sayar da fom din sha'war neman takara kafin zaben fitar da gwani.

Babagana Zulum da Mustapha Gubio
Babagana Zulum ya daga hannun Mustapha Gubio a Borno. Hoto: Dauda Iliya
Source: Facebook

A wannan rahoton, mun tattaro muku jerin gwamnonin jihohin Arewa da suka ayyana wadanda suke so su gaje su a zaben 2027.

1. An ayyana Wadada a Nasarawa

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana Sanata Aliyu Wadada, mai wakiltar Nasarawa ta Yamma, a matsayin wanda ya ke so ya gaje shi gabanin zaben gwamna na shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Bayan abin da ya faru, an haramta wa masu digirin girmamawa amfani da 'Dr' a Najeriya

Abdullahi Sule ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da masu rike da mukaman siyasa a gidan gwamnati da ke Lafia, babban birnin jihar, inda ya ce an dauki matakin ne bayan watanni ana tuntubar masu ruwa da tsaki.

“Bayan doguwar tuntuba, an rage ‘yan takarar zuwa mutum uku, wadanda aka dauka cewa kowannensu na da karfin lashe zabe. An ci gaba da tuntuba kafin daga bisani aka yanke hukunci a kan Sanata Wadada,”

In ji shi.

Gwamna Abdullahi Sule, Bola Tinubu da Ahmed Aliyu Wadada
Lokacin da Gwamna Abdullahi Sule da Ahmed Wadada suka ziyarci Bola Tinubu. Hoto: Gov Abdullahi Sule Mandate
Source: Facebook

2. An zabi Gubio a Borno

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana tsohon kwamishinansa na ayyuka, Mustapha Gubio, a matsayin wanda ya fi so ya tsaya takarar gwamna a zaben shekarar 2027.

Mai magana da yawun gwamnan, Malam Dauda Iliya, wanda ya tabbatar da lamarin ga Daily Trust, ya ce:

“Eh, Gubio ne dan takarar da Mai Girma Gwamna ya zaba, wanda ya kai masa ziyara jim kadan bayan sayen fom din takara a Abuja.”
Babagana Zulum da Mustapha Gubio
Babagana Zulum da Mustapha Gubio sun fito daga jirgi a Borno. Hoto: Dauda Iliya
Source: Facebook

3. An zabi Wali a jihar Yobe

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bayyana tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Baba Malam Wali a matsayin wanda zai so ya gaje shi.

Kara karanta wannan

APC ta fitar da dan takarar gwamna a Oyo, ta juyawa ministan Tinubu baya

Vanguard ta wallafa cewa hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da aka fitar bayan taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC ta jihar Yobe da aka gudanar a Abuja.

Masu ruwa da tsakin sun bayyana Malam Wali a matsayin gogaggen masani mai kwarewa da cancantar da ake bukata domin shugabanci da gudanar da mulki yadda ya kamata.

'Yan APC da Baba Malam Wali
Mai Mala Buni da 'yan APC sun daga hannun Baba Malam Wali. Hoto: Mamman Mohammed
Source: Facebook

4. An zabi Gwamna a Gombe

Punch ta wallafa cewa jam’iyyar APC a jihar Gombe ta bayyana Jamilu Gwamna a matsayin dan takararta na bai daya domin zaben gwamna na shekarar 2027.

Mai magana da yawun gwamnan Gombe, Ismaila Misilli ya ce an cimma matsayar ne a taron masu ruwa da tsaki karkashin jagorancin gwamnan jihar Gombe kuma jagoran jam’iyyar APC a jihar, Inuwa Yahaya.

Sai dai Legit Hausa ta rahoto cewa wasu masu neman takara da suka hada da Isa Ali Pantami da Saidu Ahmed Alkali sun nuna kin amincewa da hakan.

An daga hannun Jamilu Gwamna a Gombe
Gwamna Inuwa Yahaya ya daga hannun Jamilu Gwamna a Gombe. Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

Wadanda aka zaba a jihohin Kudu

A kudancin Najeriya, Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya sanar da Sanata Solomon Adeola mai wakiltar Ogun ta Yamma, a matsayin ɗan takarar gwamna da APC ta fi so a jihar domin zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi garkuwa da 'yan uwan mataimakin gwamna a jihar Sakkwato

Gwamnan jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu ya sanar da goyon bayansa ga mataimakinsa, Obafemi Hamzat, a matsayin wanda ya fi so ya gaje shi a zaɓen gwamnan jihar a 2027.

Obafemi Hamzat da Babajide Sanwo-Olu
Babajide Sanwo-Olu da dattawan APC sun daga hannun Obafemi Hamzat. Hoto: Babajide Sanwo-Olu
Source: Facebook

Manyan shugabannin APC a jihar Oyo sun amince da Sharafadeen Alli a matsayin ɗan takarar gwamna na bai ɗaya na jam’iyyar domin zaɓen 2027.

Shettima ya goyi bayan Wadada

A wani labarin, mun kawo muku cewa mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya nuna goyon baya ga takarar Sanata Ahmed Aliyu Wadada.

Kashim Shettima ya nuna amincewa da Sanata Wadada ne yayin wani taron tattalin arziki da aka yi a birnin Lafia na jihar Nasarawa.

Tun a baya dai Wadada ya samu goyon bayan gwamna Abdullahi Sule duk da cewa wasu 'yan jam'iyyar APC na jihar na adawa da hakan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng