Babban Makamin da Isra'ila Ta Harba Ya Fado kan Sojojinta a Lebanon
- Sojojin Isra'ila sun tabbatar da cewa sun harba makamin kariya wanda ya nufi dakarunsu da ke Kudancin Lebanon bisa kuskure
- Hukumomin Isra'ila sun kuma kama wasu 'yan mata 10 da suka tsallaka iyaka zuwa Lebanon domin kafa matsugunan Yahudawa
- Lamarin ya faru ne yayin da ake ci gaba da tashin hankali a kan iyakar Lebanon da kuma tattaunawar tsaro tsakanin ɓangarorin biyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Beirut, Lebanon – Sojojin Isra'ila sun bayyana cewa sun harba wani makamin kariya wanda ya nufi dakarunsu da ke kudancin Lebanon bisa kuskure.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce daga baya bincike ya nuna cewa abin da aka ɗauka a matsayin barazana wuta ce da sojojin Isra'ila da kansu suka yi yayin wasu hare-haren da suke kaiwa a Kudancin Lebanon.

Kara karanta wannan
Wata cuta ta rage mugun iri, ta hallaka ƙasurgumin ɗan bindiga da ya addabi jama'a

Source: Getty Images
Roya News ta rahoto cewa babu wani soja da ya ji rauni a lamarin, yayin da rundunar ta ce ta fara gudanar da bincike kan yadda kuskuren ya faru.
Mata sun tsallaka zuwa Lebanon
A wani lamari makamancin haka, hukumomin Isra'ila sun kama wasu 'yan mata 10 bayan sun tsallaka iyaka zuwa Kudancin Lebanon.
Rahotanni sun ce kusan mutum 40 ne suka yi yunƙurin shiga Lebanon, ciki har da wasu iyalai, yayin da 'yan matan suka ce manufarsu ita ce kafa matsugunan Yahudawa a yankin.
Sun shaida wa kafar Times of Israel cewa suna ganin kafa matsuguni a yankin zai taimaka wajen tabbatar da abin da suka kira nasarar yaƙin.
Isra'ila na gina sansanoni a Lebanon
Rahotanni sun kuma nuna cewa Isra'ila na ci gaba da gina manyan sansanonin soja a yankunan Kudancin Lebanon da ta mamaye.
An ce an gina sansanoni bakwai da hanyoyi masu tsawo da ke haɗa su, yayin da Ministan Tsaron Isra'ila, Israel Katz, ya umarci sojoji su gina wuraren zama kamar za su ci gaba da zama a yankin na tsawon shekaru 50.

Kara karanta wannan
Yan bindiga sun nuna rashin imani kan mata da jarirai a wani kazamin hari a Katsina

Source: Getty Images
Lamarin na zuwa ne yayin da jami'an Isra'ila da Lebanon ke tattaunawa a birnin Rome domin rage tashin hankali da kuma warware matsalolin tsaro da ke kan iyakokin ƙasashen biyu.
Abubuwan da suke faruwa a Gabas ta Tsakiya na karuwa ne a yankin tun bayan yakin da Isra'ila da Amurka suka kaddamar da hare-hare a kan Iran.
An kashe sojojin Isra'ila a Lebanon
A wani labarin, mun ruwaito cewa sojojin Isra'ila biyu da ke aikin mamaya sun rasa rayukansu yayin faɗan da suka je yi a Kudancin kasar Lebanon.
Haka kuma mayaƙan Houthi da ke Yemen sun yi ikirarin harba makaman roka masu linzami zuwa wani jirgin dakon mai na Saudiyya a Tekun Bahar Maliya, ko da yake babu wata hujja da suka gabatar.
Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da tattaunawa tsakanin Iran da Oman kan batun mashigar Hormuz, tare da shugaban Amurka Donald Trump yana hasashen cimma yarjejeniya nan ba da jimawa ba.
Asali: Legit.ng