Dalilan EFCC na Dakatar da Asusun Gwamnatin Osun kafin Zabe
- Hukumar yaku da rashawa ta EFCC ta ce ta sa takunkumi a asusun gwamnatin Osun ne domin kare kudaden jama'a daga zargin fadawa aljihun wasu
- EFCC ta bayyana cewa ana binciken gwamnatin jihar kan zargin karkatar da Naira biliyan 11 tun daga watan Maris, 2026, kuma wannan daga matakan da aka dauka
- Hukumar da ke yaki da rashawa ta musanta cewa matakin yana da alaka da zaben gwamnan Osun mai zuwa, kuma wannan ba ya nufin akwai son rai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Hukumar Yaki da Masu Yi Wa Tattalin Arziki Ta'annati (EFCC) ta ce ta dakatar da asusun bankin gwamnatin jihar Osun ne domin dakile abin da ta bayyana a matsayin karkatar da kudin jama'a.
Wannan na zuwa ne makonni kadan gabanin zaben gwamnan jihar, wanda gwamna mai ci, Ademola Adeleke ya ke sake neman takara.

Source: Twitter
A sakon da ta wallafa a shafinta na X da shugaban sashen yada labarai da hulda da jama'a na EFCC, Dele Oyewale, ya sanya wa hannu a ranar Laraba, 5 ga watan Agusta, 2026, hukumar ta ce tana gudanar da bincike kan gwamnatin jihar Osun tun daga watan Maris na shekarar 2026.
EFCC na binciken gwamnatin Osun
Jaridar Punch ta wallafa cewa EFCC ta ce binciken ya shafi zargin karkatar da kudin Asusun Muhalli, Asusun Tallafi da kuma rabon kudaden FAAC da darajarsu ta kai Naira biliyan 11.
Hukumar ta bayyana cewa ta riga ta gayyaci wasu jami'an gwamnatin jihar domin yi musu tambayoyi, ciki har da Akanta Janar na jihar.
A cewar EFCC, ba ta dauki matakin dakatar da asusun gwamnatin ba sai bayan da ta gano ana tura makudan kudi daga asusun gwamnati zuwa wasu asusun da take zargin ba su da gaskiya.
EFCC ta kare matakin ta
Ta kara da cewa binciken ya nuna an tura makudan kudade zuwa wasu kamfanoni, lamarin da ya sa ta gaggauta dakatar da karin zirga-zirgar kudaden.
EFCC ta kuma yi watsi da ikirarin cewa matakin yana da alaka da zaben gwamnan Osun da ke tafe, tana mai cewa manufarta ita ce kare dukiyar al'umma ba tare da la'akari da yanayin siyasa ba.

Source: Twitter
EFCC ta kuma bayyana cewa tana sanya ido kan harkokin kudaden wasu jihohin da ake gudanar da irin wannan bincike a kansu, tana jaddada cewa ba ta goyon bayan wata jam'iyya ko bangaren siyasa.
Hkumar ta bukaci 'yan Najeriya su yi watsi da abin da ta kira rahotannin da ba su dace ba game da matakinta, tana mai cewa za ta ci gaba da kare kudaden jama'a domin amfanin kasa baki daya.
Hukumar EFCC ta rufe asusun gwamnati
A baya, mun kawo labarin cewa hukumar EFCC ta rufe wani asusun gwamnatin Osun wanda ake amfani da shi wajen biyan albashin ma'aikata kwanaki 10 kafin zaɓen gwamna da za a yi a jihar.
Gwamna Ademola Adeleke ya ce tun da farko ya yi gargaɗin cewa ana shirin daskarar da asusun gwamnati domin kawo cikas ga ayyukan gwamnati yayin da ya rage kwanaki kadan a yi zabe.
Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na jihar, Kolapo Alimi, ya fitar inda gwamnan ya ce hakan wani yunƙuri ne na kawo cikas ga ayyukan gwamnati gabanin zaɓen.
Asali: Legit.ng


