2027: Shettima Ya Nuna Wanda Ya ke So Ya Zama Gwamnan Nasarawa
- Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya halarci taron tattalin arziki da aka kaddamar a jihar Nasarawa a ranar Laraba
- A bayanin da ya yi, Kashim Shettima ya yi kalaman da ke nuna cewa yana goyon bayan Sanata Ahmed Aliyu Wadada da ya zamo gwamna
- Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya nuna cewa yana so Sanata Wadanda ya gaje shi a 2027 duk da wasu 'yan APC sun ce suna da ja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Nasarawa - Gabanin zaben fidda gwani na gwamna na jam’iyyar APC a jihar Nasarawa, Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya yi magana kan Ahmed Aliyu Wadada.
A ranar Laraba, Shettima ya mara wa Gwamna Abdullahi Sule baya ta hanyar bayyana goyon bayansa ga Sanata Ahmed Aliyu Wadada a matsayin gwamnan Nasarawa na gaba a shekarar 2027.

Source: Facebook
Taron tattali da aka yi a Nasarawa
Kashim Shettima ya wallafa hotunan taron tattalin arziki da ya halarta a jihar Nasarawa a shafinsa na Facebook, inda ya yi magana kan Sanata Wadada.
Shettima ya yi wannan bayani ne yayin bude taron zuba jari na Nasarawa na kwanaki biyu na shekarar 2026 a birnin Lafia.
Taron shi ne na karshe karkashin gwamnatin Abdullahi Sule, kuma an mayar da hankali ne wajen tabbatar da dorewar sauye-sauyen tattalin arziki bayan zaben 2027.
Da yake jawabi ga mahalarta taron mataimakin shugaban kasar ya tabbatar wa masu zuba jari cewa tafiyar tattalin arzikin Nasarawa za ta ci gaba da kasancewa mai karko a karkashin duk wanda ya gaji Gwamna Sule.
Fatan Shettima ga takarar Wadada
Shettima ya yi addu’a tare da bayyana fatan cewa da yardar Allah, Sanata Ahmed Aliyu Wadada, wanda ya halarci taron, zai gaji Gwamna Sule tare da tabbatar da ci gaba da dorewar manufofin zuba jarin jihar.
Ya ce wannan tabbaci yana da muhimmanci wajen tabbatar da kwarin gwiwar masu zuba jari yayin da jihar ke tunkarar sauyin siyasa na 2027.
Punch ta wallafa cewa Shettima ya ce:
“Ina son tabbatar wa masu zuba jari cewa da yardar Allah, wanda yake zaune tare da mu a nan shi ne gwamnan Nasarawa na gaba. Zai mutunta duk wata yarjejeniya,”
Ya ci gaba da bayyana Sanata Wadada a matsayin gogaggen masani a harkar banki wanda kuma:
“Zai ci gaba daga inda Injiniya A.A. Sule zai tsaya.”

Source: Facebook
Daga nan sai Shettima ya juya kai tsaye zuwa ga Wadada, wanda ke wakiltar Nasarawa ta Yamma a Majalisar Tarayya kuma ake kallonsa a matsayin wanda Abdullahi Sule ke so ya gaje shi a zaben gwamna na 2027, ya ce:
“Sanata Wadada, aikin da ke gabanka a bayyane yake. Muna maka fatan alheri.”
Shettima ya gargadi 'yan APC
A wani labarin, mun kawo muku cewa mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya gargadi 'yan jam'iyyar APC kan takarar 2027.

Kara karanta wannan
Pantami ya yi martani da APC ta yi amfani da tsarin 'sulhu' a tsayar da ɗan takara
Shettima ya bayyana cewa wasu za su iya nuna fushi idan suka rasa tikitin takara a zabe mai zuwa, inda ya ce hakan zai zama babbar illa ga APC.
Ya bukaci a hada kai wajen ciyar da APC gaba a zabe mai zuwa, inda ya ce dole ne kowa ya san cewa mutum daya ne zai samu tikitin takara.
Asali: Legit.ng

