Siyasa Ta Fara Zafi, Gwamna Ya Yi Tsaurin Ido Ya Gargadi Tinubu kan Zabe

Siyasa Ta Fara Zafi, Gwamna Ya Yi Tsaurin Ido Ya Gargadi Tinubu kan Zabe

  • Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya gargaɗi shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da kada ya bari a tafka maguɗin zaɓen gwamnan jihar da za a yi ranar 15 ga Agusta
  • Adeleke ya ce duk wani yunƙurin maguɗin zaɓe na iya janyo rikicin siyasa irin wanda ya faru a shekarar 1983, yana mai cewa al'ummar Osun ba za su amince da hakan ba
  • Gwamnan ya kuma buƙaci Tinubu ya dakatar da abin da ya kira cin zarafin 'yan siyasa da jami'an 'yan sanda ke yi, tare da umartar shugabannin APC su guji tayar da tarzoma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Osogbo – Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya yi kira ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya tabbatar an gudanar da zaɓen gwamnan jihar cikin adalci da gaskiya.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Yadda aka raba N700m don kifar da gwamnatn Tinubu

Adeleke ya yi gargaɗin cewa duk wani yunƙurin yin maguɗin zaɓen ranar 15 ga Agusta na iya jawo rikicin siyasa irin wanda ya faru a shekarar 1983.

Ademola Adeleke da Bola Tinubu
Ademola Adeleke a hagu da Bola Tinubu a dama. Hoto: Bayo Onanuga|Osun State Government
Source: Twitter

Vanguard ta rahoto cewa gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayin da yake jawabi ga magoya bayansa a yankin Orita-Sabo da ke ƙaramar hukumar Olorunda a jihar Osun.

Adeleke ya aika saƙo ga Tinubu

A cewar Adeleke, shugaban ƙasa bai kamata ya zura ido yana kallon abin da ya kira rikicin siyasar da wasu jiga-jigan APC ke haddasawa a jihar ba.

Ya ce:

"Mai girma shugaban ƙasa, ina roƙonka ka kula da kalamaina. Ni ne babban mai lura da tsaro a jihar Osun, kai Bayarabe ne, Osun ma ƙasar Yarbawa ce. Duk da haka wasu shugabannin jam'iyyarka suna haddasa rikicin siyasa kana kallonsu."

Ya ƙara da cewa abin da al'ummar Osun ke buƙata shi ne zaɓe cikin 'yanci da adalci ba tare da maguɗi ba.

Rikicin siyasar 1983 a Osun

Adeleke ya ce idan aka yi ƙoƙarin yin maguɗin zaɓe, rikicin siyasar shekarar 1983 da ya biyo bayan zaɓen tsohon gwamnan jihar Ondo, Michael Ajasin, na iya maimaituwa.

Kara karanta wannan

Shin da gaske ne cewa Sarkin Musulmi ya ce a zabi Tinubu a 2027?

Punch ta wallafa cewa ya buƙaci Tinubu da ya umarci shugabannin jam'iyyarsa da kuma manyan jami'an 'yan sanda su tabbatar da zaman lafiya a jihar.

A cewarsa:

"Ka yi gwagwarmayar tabbatar da dimokuraɗiyya a Najeriya. Kada ka bari mutanenka su rusa ta. Ka tashi tsaye ka dakatar da abubuwan da ke faruwa a Osun."
Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya yana yi wa jama'a bayani. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

A nasa jawabin, Darakta Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Imole, Sanata Lere Oyewumi, ya buƙaci magoya bayan jam'iyyar su fito domin kaɗa ƙuri'a tare da kare ƙuri'unsu a ranar zaɓe.

Tinubu ya jawo muhawara

A wani labarin, mun ruwaito cewa takardun takarar shugaban ƙasa na Bola Ahmed Tinubu da INEC ta wallafa domin zaɓen 2027 sun sake tayar da muhawara kan cancantar karatunsa.

INEC ta bayyana cewa ba aikinta ba ne tantance sahihancin takardun karatu da 'yan takara ke gabatarwa kafin wallafa su domin jama'a su duba.

Takardun da aka wallafa sun nuna shaidar digirin Tinubu daga Jami'ar Chicago (CSU) da kuma takardar NYSC, yayin da wuraren da aka tanada domin shaidar makarantar firamare da sakandare suka kasance babu bayanai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng