Hankalin Trump Ya Tashi da Musulmi, Abdul El Sayed Ya Lashe Zabe a Amurka
- Shugaban Amurka Donald Trump ya caccaki Abdul El-Sayed bayan ya lashe tikitin takarar Sanata na jam'iyyar Democrat a Michigan
- Trump ya bayyana nasarar El-Sayed a matsayin albishir ga jam'iyyar Republican, yana mai sukar manufofin ɗan takarar
- Abdul El-Sayed ya yi kira ga haɗin kan jam'iyyar Democrat domin fuskantar zaɓen watan Nuwamba da zai kara da Mike Rogers
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Washington DC – Shugaban Amurka, Donald Trump, ya fara martani kan nasarar Abdul El-Sayed a zaben fitar da gwani na jam'iyyar Democrat domin takarar kujerar Sanata a jihar Michigan.
Trump ya bayyana nasarar El-Sayed a matsayin abin farin ciki ga jam'iyyar Republican, yana mai caccakar sabon ɗan takarar da zai fafata da Mike Rogers a babban zaɓen watan Nuwamba.

Source: Getty Images
USA Today ta rahoto cewa Trump ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta sa'o'i kaɗan bayan aka tabbatar da nasarar El-Sayed.
Me Trump ya ce kan El-Sayed?
A cikin saƙon nasa, Trump ya yi ikirarin cewa nasarar Abdul El-Sayed za ta amfani jam'iyyar Republican a zaɓen da ke tafe.
Ya kuma yi zargin cewa El-Sayed yana da ra'ayoyin siyasa masu tsauri, tare da kai masa hari kan matsayinsa game da Isra'ila da sauran batutuwan siyasa.
Trump ya kuma yi tsokaci kan abokiyar hamayyar El-Sayed a zaben fitar gwani, Haley Stevens, yana mai cewa yadda ta kusan lashe zaɓen ya nuna akwai rabuwar kai a cikin jam'iyyar Democrat.
El-Sayed ya nemi haɗin kai
Rahoton Anadolu ya nuna nuna cewa El-Sayed ya samu nasara da tazarar kusan kashi ɗaya cikin ɗari bayan kammala ƙidayar ƙuri'u.
Bayan sanar da sakamakon, Haley Stevens ta amince da shan kaye tare da bayyana goyon bayanta ga El-Sayed domin jam'iyyar Democrat ta haɗa kai gabanin babban zaɓen.

Kara karanta wannan
Ana wasan sauya sheka a Gombe, sakataren ADC ya yi murabus, ya kama layin Pantami

Source: Getty Images
El-Sayed, wanda likita ne kuma ƙwararren masanin lafiya, ya buƙaci magoya bayansa su manta da rigingimun zaɓen fitar da gwani su mayar da hankali kan fafatawar da za su yi da jam'iyyar Republican a watan Nuwamba.
Ga bidiyon da shugaba Donald Trump ya yi magana da shafin Clash Report ya wallafa a kafar X:
Rashida Tlaib ta ci zabe
A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yar majalisar wakilan Amurka Rashida Tlaib ta sake lashe zaɓen fidda gwani na jam'iyyar Democrat a mazabar Michigan ta 12.
Rahotanni sun bayyana cewa nasarar Rashida ta ci gaba da nuna ƙaruwar tasirin masu ra'ayin sassauci da kawo ci gaba a cikin jam'iyyar Democrat a jihohin Amurka.
Rashida Tlaib da Alexandria Ocasio-Cortez na daga cikin fitattun 'yan siyasar da suka yi fice saboda manufofinsu na kawo sauyi tun bayan shigarsu majalisar dokokin Amurka a shekarar 2019.
Asali: Legit.ng
