Takarar Gwamna: Sheikh Isa Pantami Ya Yi Maganar Sauya Sheka daga APC
- Sheikh Isa Ali Pantami na cigaba da maganganun da ake nuna kin amincewa da yadda aka fitar da 'yan takarar APC a jihar Gombe
- Ya bayyana cewa bai gamsu da hanyar da shugabannin APC suka bi wajen zaben Jamilu Isiyaku Gwamna a matsayin dan takara ba
- Pantami ya yi magana game da yiwuwar sauya sheka daga APC zuwa wata jam'iyya da aka masa tambaya kan matakin da zai dauka
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Gombe - Fitar da 'yan takara da Gwamna Inuwa Yahaya da jam'iyyar APC suka yi a jihar Gombe na cigaba da tayar da kura a fagen siyasa.
Tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Pantami na cikin wadanda suke kalubalantar hanyar da aka bi wajen fitar da 'yan takarar.

Source: Facebook
A wata hira da tashar BBC Hausa da aka wallafa a Facebook, Sheikh Isa Pantami ya ya amsa tambaya kan yiwuwar sauya sheka idan ba a masa adalci ba.
Maganar sauya shekar Sheikh Isa Pantami
An yi wa Sheikh Pantami tambaya kan cewa ko zai sauya sheka domin samun damar takara idan bai samu tikitin APC a jihar Gombe ba, sai ya ce:
"Muna da matakai guda uku a yanzu nan gaba, lokacin bayyana su bai yi ba, za mu bayyana. Muhimmi abu a yanzu shi ne har yanzu mu 'yan jam'iyyar APC ne."
Da aka tambaye shi ya ko Jamilu Isiyaku Gwamna da Inuwa Yahaya ya zaba ya tuntube shi, Pantami ya sanar da cewa shi ba ya rikici da kowa, kawai yana fada da zalunci ne.
Pantami ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu
A yayin hirar da aka yi da shi, Sheikh Isa Ali Pantami ya bayyana cewa ya tattauna kai tsaye da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan batun fitar da 'yan takara a 2027.
"Na ji dadin maganar da shugaban kasa ya yi, da ya ce bai yarda a yi kama-karya ba, kuma wannan magana, ni ya kira ni ya fada min babu shamaki.

Source: Facebook
Baya ga haka, Pantami ya bayyana cewa Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya tabbatar da cewa bai yarda a yi kama karya ba.
Ya ce:
"Na biyu, shugaban jam'iyya na kasa, Farfesa Nentawe ya ce bai yarda a yi kama karya ba. In akwai mutum daya da ya ga ba a masa adalci ba kuma ya cika sharuda za a je a yi 'yar tike.
Pantami ya bayyana cewa abin da suka yi sun cancanci a yaba musu, inda ya bayyana cewa yana sukar lamarin ne domin a yaki zalunci.
Ga bayanin da Pantami ya yi a bidiyo a kasa:
An tarawa Pantami kudin fom
A wani labarin, kun ji cewa magoya bayan Sheikh Isa Ali Pantami sun yi gangamin tara kudi domin saya masa fom din neman takarar gwamna a Gombe.
Shugaban kwamitin tara kudin ya sanar da cewa masoya malamin daga ciki da wajen jihar Gombe sun tara masa sama da Naira miliyan 50.
Wasu daga cikin mutanen da Sheikh Pantami ya samawa ayyuka a Najeriya na cikin wadanda suka tura masa gudunmuwar kudi.
Asali: Legit.ng

