Gwamnan Bauchi na Neman INEC Ta Sauya Jadawalin Zaben 2027 domin Musulmai
- Gwamna Bala Mohammed ya bukaci a la’akari da lokacin aikin Hajjin bana wajen tsara zabuka da sauran manyan ayyukan siyasar 2027
- Ya nuna damuwa cewa Musulmai da dama masu shiga harkokin siyasa ba za su samu damar shiga aikin Hajjin bana yadda ya kamata ba
- Bala Mohammed ya yi wannan kira ne yayin jawabinsa na bankwana da maniyyata a sansanin Alhazan Sultan Sa’ad Abubakar a jihar Bauchi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya ce rashin dacewa ne yadda jadawalin zaben 2027 da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta fitar ya yi karo da lokacin aikin Hajji.
Bala Mohammed ya soki INEC kan tsara ayyukan zaben 2027, yana mai bayyana rashin dacewa yadda muhimman zabukan fitar gwani na jam’iyyun siyasa za su yi karo da lokacin hawan Arafa.

Source: Twitter
Arise News ta wallafa cewa gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin bikin bankwana da maniyyata Musulmi a sansanin Alhazan Sultan Sa’ad Abubakar da ke Bauchi.
Korafin Gwamnan Bauchi kan jadawalin zaben 2027
Bala Mohammed ya nuna damuwa cewa ‘yan siyasa Musulmi da masu ruwa da tsaki da dama da ke son zuwa aikin Hajji ba za su samu damar tafiya ba saboda ana sa ran zabukan fitar gwani na jam’iyyu za su yi daidai da lokacin Arafa.
A cewarsa, wannan karo tsakanin jadawalin zabe da daya daga cikin mafi muhimmancin ibadun Musulunci bai yi la’akari da yawan Musulman Najeriya ba.
“Ina kira ga NAHCON da ta duba abin da shugaban majalisa ya fada. Yawancinmu ba za mu iya tafiya ba kuma rashin tunani ne dukkan ka’idojin zabe da dokar zabe ba su yi la’akari da lokacin Hajji ba saboda yawancin ‘yan Najeriya Musulmi ne...”
in ji shi.
“Kusan ranar da za mu yi Arafa ita ce ranar da yawancin jam’iyyun siyasa za su yi zabukan fitar gwani. Wannan ba abin yarda ba ne.”
2017: Kira a sauya jadawalin INEC
Gwamnan ya roki Shugaba Bola Tinubu, Majalisar Tarayya, Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON), da INEC da su yi la’akari da kara wa’adin jadawalin domin bai wa shugabannin siyasa Musulmi da maniyyata damar gudanar da aikin Hajji.
Ya ce:
“An yi wannan roko ne da kyakkyawar niyya ba saboda siyasa ba, sai don tunatar da shugabanninmu cewa muna da hakkin kula da dimbin Musulmanmu,”
Radio Nigeria ya rahoto ya ce Mohammed ya kuma bukaci maniyyatan da su yi addu’ar zaman lafiya, tsaro, ci gaban tattalin arziki da hadin kan Najeriya yayin da suke kasa mai tsarki.

Source: Facebook
Gwamnan ya kuma karfafa wa maniyyatan guiwa da su kara kusantar Allah tare da taimaka wa sauran alhazai, musamman tsofaffi da masu bukatar taimako.
Gwamnan Bauchi zai yi takara a 2027
A wani labarin, mun kawo muku cewa Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya bayyana cewa zai yi takara a zaben 2027 da ke tafe.
Bala Mohammed ya sanar da haka ne yayin da ya ke karin bayani kan dalilan da suka sanya shi barin jam'iyyar PDP duk da shafe shekaru a cikinta.
Gwamnan ya kara da cewa yawancin 'yan siyasar da suke tare da su a wasu jihohin Najeriya za su sauya sheka domin samun damar takara a 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


